Tuesday, 17 March 2020
Daga Karshe Sarkin Waka Nazir M Ahmad Ya Fadi Matsayinsa Na Sarkin waka san Kano (karanta)

Home Daga Karshe Sarkin Waka Nazir M Ahmad Ya Fadi Matsayinsa Na Sarkin waka san Kano (karanta)
Ku Tura A Social Media
Fitaccen mawakin Hausar nan, Nazir M. Ahmad, yayi murabus daga sarautar sa ta Sarkin Wakar Sarkin Kano.
Cikin wata sanarwa da Nazirun ya sanyawa hannu mai dauke da kwanan watan ranar 13, ga watan Mayun da muke ciki, Naziru ya ce ya ajiye sarautar nan take.

Sannan yayi godiya ga masarautar Kano bisa bashi wannan sarauta da ya shafe shekara guda akan ta.

Idan zaku iya tunawa dai a watan Disamba na shekarar 2018 ne, Sarkin Kano na wancan lokacin Muhammadu Sanusi II ya nada Nazir M. Ahmad matsayin Sarkin Wakar Sarkin Kano.
Naziru M. Ahmd yayi suna wajen wakar sarakuna.


Wakar sa mai farin jini da ya yiwa Sarkin Kanon na wancan lokaci ita ce “Mata ku dau turame” wadda har yanzu jama’a ke cigaba da yayin ta, ta yadda akan sanya wakar a mafi yawan bukukuwa da ake gudanarwa a kasar Hausa, kamar yadda wani rahoton BBC Hausa ya bayyana a makon da ya gabata.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: