Thursday, 19 March 2020
Coronavirus Ba sabon Abu Bane - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Karanta Bayyani Dalla Dalla)

Home Coronavirus Ba sabon Abu Bane - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Karanta Bayyani Dalla Dalla)
Ku Tura A Social Media

An dade ana gamuwa da ibtila'i da jarrabawa a fadin duniya, kwalara da Annoba da yaduwar cutaka ya dade yana addabar duniya, Kuma ana yi masa farrasa iri iri, kowa gwargwadon abinda yake dauke da shi na akida, ko hankali, ko ilmi ko al'ada, ko surkulle.

Amma mu a mahanda ta addini muna daukar wadananan a matsayin jarrabawa da Jan kunne da Allah yake yiwa mutane domin su saduda, su sallamawa Allah, su yadda wananan duniya akwai me ita, Kuma yana da iko akanta kuma zai Iya tashin ta duk sadda yaga dama.

Domin abubuwan da ake aikatawa a wananan duniya na masha'a sunyi yawa, butulci da kangarewa, da shishigi yayi yawa, wasu ma basu yadda akwai Allah ba, wasu Kuma sun yadda akwai Allah amma sun bashi siffofi irin na mutane, wasu kuma sun yadda da Allah amma sun bijirewa dokokinsa, wasu kuma sun takale shi da fada ta hanyar fada da Annabin sa, da muzantashi, da yiwa addinin sa izgili da baa,
Wasu sun shagala da duniya sun manta da lahira, wasu kuma suna kokarin kwatanta abinda Allah ya yi umarni gwargwadon ikon su.

Wananan duka ba zai hana samun jarrabawa ba daga lokaci zuwa lokaci, Kuma akan kowa da kowa, watakila wani yace to mai yasa abin yake shafar musulmi da mutanan kirki, ba ya tsayawa akan Iya wadanda suka jawo shi, amsa shine ita jarrabawa tana shafar kowa, amma ga mumini sai ya zama shahada da kaffara, ga kafiri sai ta zama azaba da gargadi, ga fasiki Kuma sai ya zama izna da waazi, ga misali na wasu Annoba da aka samu a duniya a tsawon tarihi,
An yi wata Annoba a shekara ta 18 Bayan hijra, 640 miladiyya, lokacin kalifancin S. Umar, a wani yanki na kasar Sham, Mai suna Amwas, wadda ta halakar da mutane kusan dubu 20, daga ciki har da wasu manyan sahabbai kamar Abu Ubaidatu Bn Jarrah da Muazu Dan jabal,
1, Annoba a akayi a yankin Germany zuwa Rum a shekara ta 165 Har zuwa 180, adadin mutuwa mai yawan gaske .

2 wata Annoba da aka yi a yankin Asiya zuwa Africa a tsakanin shekara ta 541 zuwa 542, wanda aka yi hasarar rayuka Masu yawa.
3, wata mummunar bakar Annoba wacce aka yi a shekara ta 1346, zuwa 1353, wacce ta fara daga turai ta shiga yankin Asiya, Har zuwa Africa, wananan cuta ta yadu ta hanyar kudin cizo har aka yi hasarar rayuka masu tarin yawa , wanda duniya ta girgiza  a  lokacin.

4. Annobar Landon wacce aka yi ta a shekara ta 1665 zuwa 1666 miladiyya, wacce aka bayar da rahoto cewa mutum sama da dubu dari suka sheka lahira.
5.  Wata Annoba a yankin Faransa a shekara ta 1720 wadda ta halaka sama da mutum dabu dari.

6.  Wata Annoba da ta barke a yankin Amurka a shekarar 1793, ta kashe sama da mutum dabu 40,
7. Wata cuta mai suna kwalara a shekarar 1820 wacce ta fara daga kudu maso gabashin Asiya ta kashe mutane da dama wadda ta fara daga wani kauye a cikin India har ta kusa gamai duniya.
8. Wata Annobar daga kasar sin a shekara ta 1910 zuwa 1911, ta kashe sama da mutum dubu 60.

9. Sai wacce akayi a Honkon 1968 a tsawon kwana 17 wadda ta kashe kusan miliyan daya.
10. Sai Cutar HIV mai karya garkuwar jiki wacce ta fara daga 1976, har yau ana fama da ita, Allah kadai yasan yawan wadanda ta kashe zuwa yanzu.

11. da wacce akayi mata suna zika, wanda ya yadu a Brazil, yana kama Yara ta hanyar cizon sauro, yayi barna a kusan kasashe 68, 2015.

12. Ciwan mashasharar aladu 2009, wanda ya faro daga Mexico ya yadu yayi Barna a duniya har zuwa 2010.

13. Ibola wani ciwo kuma Annoba 2013 ya faro daga wani yanki anan Afrika, farkon tashin sa ya kashe kusan mutum dubu 6.

14. Ga kuma lassa kwanan nan.
15. Ga kuma Coronavirus, Allah kadai yasan me zai faru, amma ko yanzu an dauki darasi, domin wadanda basu yadda da Allah ba sunce a rokeshi ko a sami mafita, abin mamaki ace komai ya tsaya tsak a duniya, gidajan kida da rawa wasanni, Mashaya,
16. Kuma mutane suna kaura daga yankin Afrika suna zuwa turai, domin gudun talauci, amma yanzu turawa suna gudowa daga turai zuwa Afrika domin gudun Coronavirus,
17. Muyi abubuwa biyar
18. Na daya yadda da kaddara Mai dadi da Mara dadi duk daga Allah ne
19. Mu dauki matakan kare kai yadda jamian kiwan lafiya suke fada
20. Mu dukufa da tuba da istigfari da komawa ga Allah, domin ya yaye mana wananan Annoba, da yawaita zikri da addua.
21. Duk musulmin da ya mutu yayi shahada,
22. Kada mu shiga inda Annoba take, Kada kuma mu fita daga inda ake yi har sai an tabbatar da bamu dauka ba.
23. Allah ya fidda mu lafiya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: