Kannywood

Na Koyi Darasi A fim Dina Na Farko – Jaruma Asabe Madaki

Daya daga cikin jaruman Kannywood mata wanda ke tashe a yanzu a masana’antar fina-finan Hausa da na turanci Asabe Madaki ta bayyana ilimi da karuwar da ta samu a fim din ta na farko a Kannywood mai suna “SARAUNIYA”.

Jarumar ta bayyana hakan ne lokacin da suke tattaunawa da majiyar mu dangane da Kannywood da kuma abun da ya jawo hankalin ta na fara fitowa a fina-finan Hausa.

Inda ta fara mana da cewa” da farko dai ina godiya ga gwamnatin jihar kaduna da jihar Kano a kan irin gudummawar da suke bayar wa ga masana’antar fina-finan Kudu da na Arewa. Kuma kafin na fara yin waka da shirin fim ni babbar lauya ce, na yi karatun lauya kuma yar kasuwa ce ni, kuma ina da kamfanin daukar shirye-shirye nawa na kai na wanda yanzu haka ina kokarin na ga na fara bada umarni da kuma daukar nauyin shirye-shirye a nan ba da jimawa ba. A fannin fim dina kuwa a gaskiya na samu ilimi da karuwa sosai a fim din da na fara fitowa a Kannywood mai suna SARAUNIYA duk da cewa ba shi ne fim di na ne farko ba a duniya, amma ya zama daya daga cikin fina-finan da nake alfahari dasu, kasancewar shi fim mai ma’ana wanda ya ke dauke da darussa tare da fadakarwa da yawan gaske a cikin sa. Abun da shirin ke kunshe da shi kuwa shi ne, na farko an kara tunatar da ni a kan ‘ya’ya mata suma za su iya daukar duk wani abun da namiji zai dauka a rayuwa, kamar mulki, gadon gida ko kuma kula da wata dukiya na iyayen ta indai  har an bata tarbiyya mai kyau kuma an nuna mata abubuwa da yawa. Toh zata iya kulawa da komai kamar yadda namiji zai yi tun da ita mutun ce kamar kowa.” A cewar Asabe Madaki.

Ta kara da cewar”Shirin Sarauniya ya kara wayar da mutane kai a kan su dai na mayar da yara mata gefe a fannin mulki ko wani mukami saboda yin ba dai dai, duk wani abun da da namiji zai yi mace ma za ta iya yi watakil fiye dashi. Kuma shirin ya nuna cewa zaman lafiya abu ne mai kyau, duk wani abun da kaga Allah ya baiwa wani toh ba wanda ya isa ya kwace maka saboda Allah ne ya baka duk wuya duk rintsi naka ne. Kuma mutun ya zama adalin shugaba a kan duk wani mukamin da Allah ya bashi. Kuma ina farin ciki a kan irin cigaban da Kannywood ta samu a yanzu saboda kullum suna kokarin gyara fina-finan su, saboda yanzu muna shiga manya gasar fim ta duniya da fina-finan mu, toh dalilin hakan yasa kowa ya ke kan jiki kan karfi wajen gyara aikin sa. Kuma Kannywood za ta kai inda ba a taba tsammani ba wasu daga cikin cigaban suna, nan gaba za a samu jarumai masu ilimi, manyan sinimomi, manhajoji na kallon fim a duniya da kuma abubuwa da daman gaske”. Inji Jarumar.

Daga karshe ta yi wa masoyan ta godiya tare  da fatan alheri da kuma albishir a kan cewa nan gaba za ta yi kokari ta kawo masu  duk abun da suke so tare da sababbin wakoki masu fadakarwa da nishadantar wa da za ta yi a nan gaba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button