Saturday, 22 February 2020
Misbahu M Ahamd Ya Fadi Yadda Yan Kannywood Zasu Samu Mafita

Home Misbahu M Ahamd Ya Fadi Yadda Yan Kannywood Zasu Samu Mafita
Ku Tura A Social Media
A SAKAMAKON taɓarɓarewar al'amura da ke wanzuwa a masana’antar finafinan Hausa, wani kwamiti da 'yan fim ɗin su ka kafa ya ɗauri aniyar yin gangamin yin addu'o'i tare da azumi domin ceto masana'antar.fimmagazine na ruwaito.

Shi dai wannan kwamitin mai suna Kwamitin Addu'a, fitaccen mawaƙi kuma jarumi Misbahu M. Ahmad da Salisu Officer ne su ka kafa shi.

A lokacin da ya ke bayyana wannan ƙudiri, Misbahu ya yi kira ga ‘yan fom baki ɗaya da su samu lokaci a cikin wannan rana mai albarka ta Juma’a su yi addu’o’in samun mafita daga fitintinun da su ka dabaibaye masana’antar.

Misbahu ya yi wannan kira ne a cikin wani saƙon murya da ya ɗauka ya tura a yau a guruf-guruf na masana’antar da ke soshiyal midiya.

A saƙon mai tsawon minti 4 da sakan 49, an ji Mibahu ya na cewa, “Yan’uwa zan yi amfani da wannan dama in ɗan yi tambihi a kan wani abu.

"Dukkan mu dai Allah ya taimake mu aƙidar mu guda ɗaya ce, shiriyar mu guda ɗaya ce, ita ce addinin Musulunci, kuma addinin nan mun san ta inda Allah ya fito mana da shi.

"Allah ya aiko mana Annabi Muhammad, kuma mun san waye Annabi Muhammad a wurin Allah, mun san matsayin sa, mun san kusancin sa da Allah, wani abin ma Allah ne ya bar wa kan sa sani.

"Allah ya fifita Annabi Muhammadu a kan dukkan wata halitta. Sannan Allah ya yi wa halittun sa gaba ɗaya gata da Annabi Muhammadu (S.A.W), sannan Allah da kan sa ya na yi wa Annabi Muhammadu salati, kuma ya umarce mu mu yi masa.

"To abin da na ke so na nuna mana shi ne yau Juma’a ce. Wannan rana ita ce Allah ya fifita a cikin kowanne yini a cikin sati. Ina so in yi amfani da wannan dama in yi kira a gare mu, masu wannan sana’a ta harkar fim a ƙarƙashin wannan tafiya ta Kannywood, mu yi amfani da wannan dama mu fake a bakin fadar Ma’aiki (S.A.W.), mu ƙudirci wannan rana mu sa niyyoyin mu da mu ka sa a gaba na addu’a da neman mafita, Allah ya nema mana mafita a cikin wannan sana’a tamu, ya kuma ba mu ikon aiwatar da ita in mun gan ta, ya kuma dafa mana ya sa mana arziƙi a ciki mayalwaci.

"Allah dukkan wani makirci da zalunci da duk wani abu da ya ke damun mu na wannan sana’a, Allah lalata shi ya rusa shi. Allah ya karya maƙiya wannan sana’a, ya kuma shiryar da ita kan ta masana’antar, ya kuma ɗora mu a kan shiriya.

"Don haka na ke so na faɗa mana daga nan zuwa bayan Juma’a in ka samu lokaci, amma al’muhimmi shi ne mu bari a yi sallar La’asar, duk ɗan wannan masana’anta ya ƙudirci niyya, idan ka na yi wa Annabi salati sau dubu ɗaya duk ranar Juma’a, mu na roƙon da ka ƙara ya zama dubu da ɗari ɗaya; ɗari ɗayan nan ka yi tawassuli ya zama 'opening' na wannan masana’anta.

"Ka sa niyyar wannan salati ɗari da ka yi hadiyya ce ga wannan addu’o’i da za mu fara, ya zama mabuɗi, niyyar mu ta haɗu gaba ɗaya a cikin wannan rana mai albarka na duk abin da mu ka roƙi Allah, Allah ya yi mana.

"Idan mu ka roƙi Allah wani na  sharri zai cutar da mu, Allah kada ka amsa, ka juya mana shi ya zama alheri saboda Kai ne alimulgaibi.

"Dukkan buɗi da mu ke nema Allah Ka buɗe mana ƙofofin don Annabi Muhammadu.

"Dukkan tsari da mu ke nema, Allah Ka kare mu da kariyar Ka don Annabi Muhammadu.

"Da wannan na ke kira ga mutanen mu, daga bayan La’asar har ka kwanta bacci, ka samu dama ka yi mana haddiya na salati.

"In ɗari ka ke yi, ka yi ɗari da ɗaya, ɗayan nan ka bar mana shi haddiya ne, ka sa niyya a kai.

"Allah ya karɓa don wanda ake yi wa salati a wannan rana mai albarka!"

'Yan fim da dama sun yi na'am da wannan shawara da Misbahu ya kawo.

Ɗaya daga cikin su, furodusa Hassan Zain Ahmad, ya bada sanarwa cewa a ranar Litinin mai zuwa, 24 ga Fabrairu, 2020 za su buƙaci dukkan mutanen da su ke cikin wannan masana’anta da su ɗauki azumi tare da niyya a kan samun taimakon Allah da samun mafita da ci-gaba a cikin masana’antar ta Kannywood.

Ya ce: "In Allah ya yarda, ranar Litinin za mu tashi da niyya a kan mu yi wannan azumi.

"'Ya'yan mu da matan mu da iyayen mu da dukkannin masoyan mu za mu tashi da wannan addu'ar a kan Allah ya kawo mafita a Kannywood. Uban

Share this


Author: verified_user

0 Comments: