Monday, 3 February 2020
Kira Ga Mai Alfarma Sarkin Musulmai kan Wannan Dan Ta'adda Akan Kalaman Femi fani kayode - Datti assalafy

Home Kira Ga Mai Alfarma Sarkin Musulmai kan Wannan Dan Ta'adda Akan Kalaman Femi fani kayode - Datti assalafy
Ku Tura A Social Media

Kamar yadda Allah Ya tona asirin 'dan ta'addan Boko Haram Nathaniel Samuel a jiya Lahadi lokacin da yayi yunkurin tayar da bomb a cocin 'yan uwansa mabiya addinin kirista a garin Kaduna..

Sai gashi tsohon Minista Femi Fani Kayode da sauran miyagun mutane irinsa wanda suke addini daya yana kokarin nesantar da wannan 'dan ta'adda daga cikin addininsu na kirista, sannan yace wai Musulmi ne kuma Hausa Fulani, wai tilastashi akayi don ya fadi cewa shi kirista ne

Wallahi wannan maganar da Femi Fani Kayode yayi zunzurutun karya ne da sharri da kuma batanci, domin babu shakka wannan 'dan ta'addan ba Musulmi bane kirista ne, ya fito daga jiharmu ta Bauchi

Asalinsa 'dan garin Pankshin ne a jihar Pilato, garinsu yana kan iyaka da karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi, yawanci mutanen Pankshin da suke kauyuka suna iyaka da Tafawa Balewa , kasuwanci da auratayya ya hadasu sun zama daya, mutanen Tafawa Balewa suna iya samun indijin na Pankshin hakanan mutanen Pankshin kan samu na Tafawa Balewa, wannan shine yadda akayi wannan 'dan ta'addan ya zama 'dan Bauchi, amma asalinsa da iyayensa daga Pankshin ne a jihar Pilato

Yau dinnan a nan cikin garin Bauchi na hadu da 'dan garin Tafawa  Balewa wanda ya san wannan 'dan ta'addan farin sani, bashi da alaka da Musulunci ta kowace fuska, mabiyin addinin kirista ne

Kuma ba yau aka fara kama kiristoci 'yan ta'addan Boko Haram zasu tayar da bomb a coci ba, an kama da yawa a baya, anan cikin garin Bauchi an kama wata kirista zata tada bomb a coci dake Yelwan Tudu, haka nan a cocin Madalla dake garin Toro an kama wasu kiristoci zasu tayar da bomb a coci

Ya dace Mai Alfarma Sarkin Musulmai da kungiyoyin addinin Musulunci su kalubalanci Femi Fani Kayode akan sharri da kokarin boye gaskiya game da sha'anin wannan 'dan ta'adda, ya kamata a maka tsinanne a kotu ya kare kansa imba hakaba ya fuskanci hukunci

Duk wani shugaba Musulmi da Allah Ya bashi iko yake da alhakkin ya kalubalanci wannan batancin da arne Femi Fani Kayode ya yiwa Musulunci amma yayi shiru to wallahi yaci amanar Musulunci, kuma sai Allah Ya jarrabeshi kowaye, ba zamu zauna kullun ana yiwa Musulunci sharri da batanci ba sai muyi shiru saboda tsoro , shiru akan magana irin wannan cin amanar addini ne

Yaa Allah Ka kare addinin Musulunci da Musulmai daga sharrin masharranta

Share this


Author: verified_user

0 Comments: