Monday, 10 February 2020
Fim din Kannywood hudu sun shiga jerin kyautar AMVCA award

Home Fim din Kannywood hudu sun shiga jerin kyautar AMVCA award
Ku Tura A Social Media
A ranar Alhamis din nan ne ta 6 ga watan Fabrairu, gidan talabijin na Africa Magic ya fitar da jerin sunayen fina-finai na masana’antar Afrika da za a zabi fim din da ya yi fice a nahiyar Afrika ciki kuwa harda fina-finan masana’antar Jaridar Northflix Na ruwaito.

Kyautar lambar yabon ta Africa Magic Viewers’ Choice Award (AMVCAD) wanda shi ne karo na bakwai da farawa a nahiyar Afrika, kuma wanda a ke gudanarwa a jihar Legas. An dai fara bada lambar yabon ne a cikin masana’antun fina-finan Afrika a shekarar 2013, wanda ya samu karbuwa daga sassan duniyar nan baki daya.

Sai dai a wannan lokaci za a iya cewa a cikin fina-finan masana’antar Kannywood an zabi fina-finai guda hudu da suka taka rawar gani a shekarar 2019. Ga kuuma jerin sunayen fim dina-finan da a ka zaba tare da sunayen wadanda suka shirya fina-finan kamar haka:

 Tuntube - Muhammad T. Finisher

Mariya - Abubakar Bashir

Abarawa Rai - Muhammad Adam and Tundun Murtala

Sadauki - Hassan Giggs.

Sauran kyaututukan da za a bayar sun hadar da fina-finan da suka fi kyawun hoto da fitar da murya mai kyau da kwararran darakta da marubuci da dai sauran su.

Ko a shekarar da ta gabata a bangaren Kannywood fina-finan Hausa, sun shiga cikin wannan kyautar bada lambar yabon ciki kuwa harda Ali Nuhu wanda ya fito a fim din Mansoor sai fim din Umar Sanda na Kamal Alkali da Dadin Kowa sabon Salon a Arewa 24 da uwar Bari na Hamisu Lamido Iyantama da kuma Rashin sani na Tianah Johnson.

Yanzu haka dai a kalla zaben na bana na gwarzon shekarar nan a masana’antar fina-finan Afrika an zabi gurbi (28)  daga cikin su, yayin da kowa zai samu lambar yabo na gwarzon shekara wanda masu kallo ne da kansu za su zabi ra’ayin su, sannan gidan talabijin na DSTV zai haska kai tsaye wanda Linda Ejiofor daga masana’antar Nollywoodda da kuma Ibrahim Suleiman za su gabatar.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: