Saturday, 11 January 2020
Za a yi fim mai suna 'Kano' da jaruman Hausa da na kudu da na Amurka

Home Za a yi fim mai suna 'Kano' da jaruman Hausa da na kudu da na Amurka
Ku Tura A Social Media
A KARO na farko, Gwamnatin Jihar Kano za ta shirya wani katafaren fim mai ɗauke da jaruman manyan masana'antun fim na duniya, wato na Hausa (Kannywood) da na kudancin Nijeriya (Nollywood) da kuma na Amurka (Hollywood).

Manufar fim ɗin ita ce a nuna kyawawan al'adun Kano da ma Afirka baki ɗaya.

Wani mutum ɗan ƙabilar Ibo wanda ke gudanar da harkokin sana'ar fim a Amurka, Mista Ugo Muzia, shi ne ya bayyana haka a lokacin wani ƙwarya-ƙwaryan taro da aka shirya a yau Juma'a, 10 ga Janairu, 2020 a ɗakin taro na Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.

Wakilin mujallar Fim da ya halarci taron ya ruwaito babban furodusan ya na faɗin, "Dalilin da ya sa na zo garin Kano shi ne domin in gana da masu ruwa da tsaki a harkar fim na Kano da kuma hukuma domin shirin da na ke da shi na shirya fim a Kano wanda zai ƙunshi tarihi da kuma al'adun Kano da ma Afrika, har ma da baƙar fata da su ke Amurka."

Ya ƙara da cewa, "Ni ɗan Nijeriya ne, ɗan Jihar Anambra, amma ina zaune ne a ƙasar Amurka."

Mista Muzia ya faɗi dalilin sa na zaɓar Kano domin shirya wannan fim ya ce tunanin hakan ya fara ne kamar shekara uku da su ka gabata lokacin da ya zo Kano, wanda kuma shi ne zuwan sa na farko.

Ya ce a lokacin ya yi hoto ya tura a yanar gizo, sai wasu abokan sa su ka rinƙa cewa me ya kai shi garin Boko Haram? "Domin duk labarin da ake bayarwa na Kano na Boko Haram ne, da ƙazanta da kwatoci," inji shi.

"To ni kuma da na zo sai na ga ba haka ba ne. Kano gari ne mai tsari da kyan fasali, kuma akwai ci-gaba a Kano.

"Don haka na shiya zan yi fim a Kano domin na fito da al'adun ta."

A cewar Mista Ugo, fim ɗin da za a yi zai fito da al' adu ne sosai domin har hawan daba za a yi.

"Don haka ne ma a yanzu mu na kan ganawa da Hukumar Raya Al'adun Gargajiya ta Jihar Kano da kuma Gidan Makama domin tsara yadda za a yi fim irin na al'ada."

Dangane da jaruman da za su fito a fim ɗin kuwa, furodusan ya ce, "Jaruman fim ɗin sun haɗa da na Hollywood, Nollywood, da kuma na Kannywood.

"Kuma don fim ɗin ya karɓu a duniya, za a fassara shi da Isfaniya, Chanis, Faransanci da Siwahili."

Ya ce fim ɗin zai nuna tsantar al'adun Kano da na al'ummar kudancin ƙasar nan kuma za a nuna shi a gidajen sinima na dukkan nahiyoyi huɗu na duniyar nan.


Ugo Muzia (a hagu) da Afakallah a taron

Mista Muzia ya bayyana cewa sunan fim ɗin 'Kano'.

Da ya ke nasa jawabin, shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma'il Na'abba (Afakallah), ya ce, "Wannan abin alfahari ne ga Kano da kuma masana'antar finafinai ta Kannywood idan har aka ce an zaɓi Kano ta zama wajen da za a gudanar da wannan aikin.

"Don hakan ya dace da manufar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta samar da ci-gaba a cikin masana'antar finafinai ta Kannywood, da ma Jihar Kano baki ɗaya.

"Don haka mu na maraba da wannan aikin, kuma za mu bayar da goyon bayan da ya kamata don ganin aikin ya yi nasara, saboda ci-gaban jihar mu."

Afakallahu ya bayyana cewa, "Wannan ƙudiri ya samo asali ne daga yadda mu ka tashi tsaye wajen kawo gyara a cikin harkar fim, saboda gyaran da aka fara ne har aka hango daga nisan duniya aka zo za a yi wannan gagarumin aikin. Mu na godiya ga Allah, wannan ikon sa ne, ba iyawar mu ba."

A taƙaitaccen jawabin sa a wurin taron, fitaccen jarumi Ali Nuhu ya bayyana farin ciki kan ƙoƙarin da gwamnan Jihar Kano da hukumar tace finafinai su ke yi wajen ciyar da harkar fim gaba.

Mujallar Fim ta fahimci cewa a watan Afrilu mai zuwa Mista Muzia zai dawo Kano domin gudanar da tantance jaruman Kannywood da za su fito a fim ɗin, daga nan kuma a sanya ranar da za a fara aikin.

'Yan fim da dama da su ka halarci taron sun haɗa da Ali Nuhu, Baballe Hayatu, Sani Sule Katsina, Alhassan Kwalle, Hannatu Bashir, Hadizan Saima, Shehu Hassan Kano, Abba El-Mustapha, Lawan Ahmad, Abubakar  Maishadda, Yaseen Auwal, Nasiru B. Muhammad da sauran su.


'Yan fim a wajen taron

Share this


Author: verified_user

0 Comments: