Uncategorized

Ya yanke jiki ya sume saboda Bai samu Ganin Adam Zango Ba Bayan Ya Yi Tattaki Daga Sokoto zuwa Kaduna (Bidiyo)

Masu iya magana sun ce soyayyar gamuwar jini ce, hakan ce ta kasance da wani bawan Allah mai suna Saifullahi Sayyinna wanda ya kasance masoyi ga shahararren tsohon dan wasan nan na Kannywood kuma mawakin zamani Adam A. Zango.

Saifullahi dai ya yi tattaki ne tun daga jihar Sokoto zuwa Kaduna domin kawai yaga masoyin nasa Adam Zango.

Sai dai kuma matashin ya je har kofar gidan jarumin amma bai sami ganinsa, ana haka kawai sai ya yanke jiki fadi sumamme.

Hakan ya sa daga bisani ya samu ganin jarumin nasa harma ya nemi su yi hoto domin nunawa mutanen garinsu cewa burinsa na ganin Adamu ya cika.

Adam zango ne ya wallafa labarin tare dda hotunan da suka dauka da mutumin a shafinsa na Instagram inda ya ke cewa: “Lallai so ba karya bane__ALLAH ke daura bawansa soyayya ko yana so ko baya so!!

Wannan bawan ALLAN daga sokoto sayyinna yake, ya shigo garin kaduna domin kawai yaga Adam Zango. ALLAH da ikonsa yazo kofar gidana bai sami ganina ba sai ya yanke jiki fadi ya suma. Daga karshe dai ya sami ganina kuma har mun dauki hoto domin ya nunawa yan garinsu cewar ya ga masoyin shi ido da ido…SAIFULLAHI SAYYINNA kenan ALLAH ya bar soyayya!!”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button