Wednesday, 8 January 2020
Duk matsayin da a ka ba ni zan iya fitowa a fim - Ladidi Fagge

Home Duk matsayin da a ka ba ni zan iya fitowa a fim - Ladidi Fagge
Ku Tura A Social Media
Jaruma Ladidi Fagge wadda ta yi fice kuma a ke damawa da ita a fina-finan Kannywood a yanzu ta ce za ta ci gaba da iya kokarin ta a kan irin matsayin da a ke ba ta na fitowa a fim din Hausa ko wa ne iri Northflix ya ruwaito.

Jaruma Ladidi, ta bayyanawa majiyar mu ta Northflix a wata ganawa da ta yi da ita na musamman.

Ta ce” mafi yawancin matsayin da a ke ba ni a fim ina fitowa ne a hali mara kyau wato mara hakuri kuma dama matsayi ai guda biyu ne ko hali mai kyau ko ko mara kyau ko mai hakuri ko kuma hakuri, don haka ko wanne a ka ba ni zan yi iya kacin bakin kokarina domin dama babban abin da ake nema shi ne a yi abu ya yi daidai da ko wanne yanayi da a ka dora ka akai. Don haka ni bani da wani zabin abu na sana’a yi kaza yi kaza don haka in dai na yi kuma a ka samu abun da ake so ni shi kenan na gama bana tsayawa wai nafi son wannan ko nafi son wancan.”

Kwanaki an yi taron Bon Award inda a wata tattaunawa da a ka yi da ke an ji inda ki ke cewa za ki iya yin fim din kudancin kasar nan, ba kya ganin hakan zai iya jawo muki kalubale daga wajen ‘yan uwan ki ‘ya’ yanki dama abokan arziki da ki ke tare dasu?

Sai ta ce ” Dole akwai abun da zai iya yiwu da wanda ba zai yiwu ba, wanda bazai yiwun ba sai a guje masa ai.”

Dama ki na da sha’awar yin fim din kudancin kasarnan din ko kuwa daga baya ne kika ji kina sha’awa ko kuwa kawai duk daya ki ke gani da a kira ki da kar a kiraki?

“Duk daya ne, idan sun kirani zan yi idan kuma basu kirani ba laba’asa, ban sa a raina ba, kuma kwadaitawa kaina shi din ba sannan kuma idan na samu ba zan haramtawa kai na yi ba”. Inji Jarumar

Wane kira za ki yi ga mutane wadanda suke kyamatar jarumai musamman jaruman da su ke cudanya da ‘yan fim din kudancin kasar nan?

“Da farko dai tambaya ce, shi wanda a ka kyamata me ya yi aka kyamace shi? Babu yadda za ayi ba ka yi wani abu ba mutane su rinka kyamatar ka ko su na aibata ka, dole sai kayi wani abun wanda ba daidai ba, bana kin gaskiya ko da na ne na cikina ya yi ba daidai ba zan fada mas aba, sannan na nuna masa hanya ta yadda zai guji abin fada”.

Kin kasance jarumar dake fitowa matsayin uwa a masana’antar kannywood, sannan kina fitowa a mataki daban-daban, wane matakin ne yafi burgeki wanda ki ke fitowa?

“Ni ba ni da wani zabin abun da ake ba ni kuma ita sana’a yi ka za yi ka za don haka indai nayi kuma a ka samu abun da a ke so ni shi kenan na gama ba na tsayawa wai na fi son wannan ko na fi son wancan.” Inji Ladidi Fagge.

Daga karshe wane kira za ki yi wa sauran jarumai?

Inda ta ce “Ni kira na ga jarumai maza da mata yara da kuma manya da su zo mu hada kai kamar yadda ‘yan Nollywood su ke mu zama tsintsiya madaurinki daya. Domin ance sai bango ya tsage kadangare ya ke samun kafar shiga. Sannan mu ci gaba da addu’a Allah ya daukaka masana’antar mu ya kuma yi mana jagora“. A cewar Jaruma Ladidi Fagge.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: