Thursday, 2 January 2020
Budewa da Bismillah: Amal Umar za ta zama jarumar Kannywood ta farko da Za ta Fara Aure a wannan shekarar

Home Budewa da Bismillah: Amal Umar za ta zama jarumar Kannywood ta farko da Za ta Fara Aure a wannan shekarar
Ku Tura A Social Media
Majiyar ta tabbatar da cewa dukkan shirye-shirye da ya danganci bikin auren jarumar ya kammala amma ta boye ne har sai ana gab ta sanar
- Kamar yadda bincike ya nuna, jarumar zata auri wani fitaccen dan kwallon kafa ne don sun dade suna soyayya dashi
Sananniya kuma fitacciyar matashiyar jaruma, Amal Umar za ta yi aure a wannan watan na Janairu 2020, in ji wata kwakwarar majiya da ta sanar wa mujallar Fim.
Majiyar, wadda ke da kusanci da jarumar, ta tabbatar mana da cewa duk wani shiri na bikin ya kammala.
“An fitar da ranar 27 ga watan janairu don daura auren Amal tare da wani saurayi da ta dade tana soyayya dashi,” cewar majiyar.

Majiyar, wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta tabbatar wa da mujallar Fim cewa Amal ta na boye maganar bikin nata ne har sai ya rage kwanaki kadan sannan duniya ta sani. Binciken mujallar Fim din ya gano cewa, matashiyar jarumar zata auri wani fitaccen dan kwallon kafa ne. Sun dade suna soyayya da shi, don haka ga duk wanda ya san alakarsu, to yin aurensu ba wani abun mamaki bane.
Da yake Amal tana nuku-nuku da maganar auren nata, kokarin mujallar Fim tayi magana da ita ya gagara.

Wakilin mujallar fim ya kira sau da yawa a waya amma ba a samunta. Hakazalika bata mayar da martanin sakon kar ta kwana da aka tura mata ba.
Idan zamu tuna, cikin kwanakin nan ne jarumar ta dawo daga aikin Umrah. Tana daga cikin matasan ‘yam mata da suka shiga harkar fim din da kafar dama, domin cikin kankanin lokaci ta fito a manyan fina-finai da suka daga sunanta.

 Da yake jarumar ta iya turanci, ta sake yin suna a wasu manyan fina-finan Kudancin Najeriya wato Nollywood.

Share this


Author: verified_user

1 comment: