Addini

Audio : KAR KU BARI A BAKU LABARI : Dambarwa ke Faruwa Gabas Ta Tsakiya – Dr Muhammad sani Umar Rijiyar lemo

Ash-sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemj yayi cikakken bayani da fashin baki akan siyasar duniya musamman gabas ta tsakiya, da tasirin Kasar Iran, da irin zalunci da ta’addanci da barnan da shugaban sojojin Iran Janar Qassem Suleimani yayi a doron kasa kafin hallakarsa.
Malamin yayi cikakken bayani akan alakar sirri dake tsakanin Amurka da Iran da irin yadda suke taimakon juna
-Ina wanda ke son sanin dalilin da yasa Amurka ta kashe Qassim Suleimani, da kuma shin za’a iya yin yaki tsakanin kasar Amurka da Iran?
-In wanda ke son sanin irin ta’addancin da Kasar Iran take yi a Kasashen Musulmai da yadda kasashen turawa suke yiwa yaransu da suka raina?
-Ina wanda ke son sanin waye shugaban sojojin juyin juya hali na Kasar Iran Janar Qassim Suleimani da irin mugun ta’addancin da yayi a doron duniya kafin ya hallaka?
Amsoshin wadannan tambayoyi suna cikin bayanin da Ash-sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Ilimi yayi jiya juma’a, a gaban jama’ar Musulmi da wasu Manyan Malamai na wasu kasashen Musulmai wadanda suka kawo masa ziyara a cikin masallacin da yake gabatar da tafsirin Qur’ani a birnin Kano
Shine shafin Hausaloaded ya dora wannan domin ku saurari yadda mallam yayi bayyani tiryan tiryan.
Muna rokon Allah Ya sakawa Malam sakamako da gidan Aljannah, Allah Ka karawa ‘dan ta’adda Qassem Suleimani azaba da ukuba a cikin kabarinsa, Allah Ka tsare mutanen duniya daga sharrin Amurka da Iran
Sai ku latsa wannan link na kasa domin saukar da audion.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?