Wednesday, 8 January 2020
Alherin Allah Ya Kaiwa Jaruma Rahama Sadau (A Cikin Hotuna)

Home › › Alherin Allah Ya Kaiwa Jaruma Rahama Sadau (A Cikin Hotuna)

Post By:

Ku Tura A Social Media


Jaruma Rahama Sadau ta kaddamar da wata gidauniya da za'a tara kudi don sayen rigunan sanyi wanda za'a rabawa 'yan uwa Almajirai, marayu da sauran mabukata

Alhamdulillah wannan baiwar Allah ta samu nasaran yin abinda tayi niyya, wanda yanzu haka an rabawa Almajirai da marayu kayan sanyi har ma da mayukan shafawa don tausayawa da jinkai garesu

Wallahi haka zakaga Almajirai suna yawon bara babu rigan sanyi a jikinsu, sunyi fari fat fatar jikinsu na tsagewa saboda babu mayin shafawa, abinda Rahama Sadau tayi jihadi ne babba, muna jinjina da yabo gareta, kuma ya kamata ya zama abin koyi yaremu

Daga karshe muna mata fatan alheri, Allah Ya albarkaci rayuwarta, Ya kareta daga sharrin zamani, Ya saka mata da Aljannah Madaukakiya Amin.

Ga Hotunan tabbatarwa nan.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: