Friday, 6 December 2019
Rashin kirkirar sabbin masarautu a Kano shi Ya fi alkhairi - Sheikh Daurawa

Home Rashin kirkirar sabbin masarautu a Kano shi Ya fi alkhairi - Sheikh Daurawa
Ku Tura A Social Media
Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Aminu Daurawa ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta gudanar da kuri'ar jin ra'ayin mutanen jihar

- Daurawa ya ce, a tunaninsu barin kirkirar sabbin masarautun nan a jihar Kano zai fi zama alheri,jaridar legithausa.ng ta ruwaito.

- A ranar Alhamis ne majalisar jihar Kano din ta amince da kirkirar sabbin masarautun

Sanannen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta gudanar da kuri'ar jin ra'ayin mutanen jihar kafin kirkirar sabbin masarautun.

A tattaunawar da Shehin malamin ya yi da Hausa RFI, ya ce suna ganin rashin kirkirar sabbin masarautun shi zai fi alheri, don kauce wa wargaza kawunan al'umma.


Sai dai kash! A ranar Alhamis ne majalisar jihar Kano din ta amince da dokar kirkirar sabbin masarautun. Hakan ya biyo bayan gabatar da kudirin da Ganduje ya kara yi a gaban majalisar a ranar Litinin da ta gabata.

Bayan an karanta bukatar kashi na uku a ranar Alhamis, majalisar ta amince da hakan ya zamo doka a jihar. Duk kuwa da cewa babbar kotun jihar ta soke sabbin masarautun tare da dakatar da sarakunan da gwamnan ya nada.Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin, Labaran Abdul-Madari ya ce, manufar kirkirar sabbin masarautun, ita ce bunkasa ci gaba a fadin jihar kuma sun dau matakin domin talakawa ne.

A shekarar da ta gabata ne, Gwamna Ganduje ya kirkiro da sabbin masarautun, lamarin da ya ja ake kallon za a rage karsashin Mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.


Sabbin masarautun sune: Bichi, karkashin Aminu Bayero; Rano, karkashin Tafida Abubakar-Ila; Karaye, karkashin Ibrahim Abubakar sai kuma Gaya, karkashin Ibrahim Abdulkadir.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: