Uncategorized

Mu muka haifi Kannywood –Inji Kamaye

Fitaccen jarumin nan Dan’azimi Baba wanda akafi sani da Kamaye ya bayyan cewa sune suka tsungunna suka haifi masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood,dalafm na ruwaito

Yayin wata tattaunawa da Kamaye yayi da tashar Dala FM ya bayyana cewa iya tsawon shekarun da masana’antar tayi, sune suka tsugunna suka haife ta, amma rikon sakainar kashin da sukayi mata ya haifar da koma baya a masana’antar.
Sai dai yanzu zamani ya kawo cigaba wajen kayan aiki na zamani a cewar Kamayen.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da manazarta ke kallon masana’antar na fama da tangal-tangal wajen rashin tabbataccen jagoranci.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *Back to top button