Thursday, 5 December 2019
Karanta Martanin Budurwa Ronaldo Bayan Messi Ya Lashe Ballon d'or

Home Karanta Martanin Budurwa Ronaldo Bayan Messi Ya Lashe Ballon d'or
Ku Tura A Social Media
Bayan da Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Duniya ta Ballon d'Or, Masoya Babban abokin takararshi, Ronaldo ba su ji dadi ba, inda har daga cikin iyalan Ronaldon aka samu kanwarshi ta fito tana kareshi. Hakanan a wannan karin an samu Budurwarshi itama ta fito tana kareshi.


Budurwar ta Ronaldo,Georgina Rodriguez ta fito ta shafinta na Insgaram inda take bayyana cewa Ronaldo ya lashe kyautukan kwallo da dama kuma yaci kofuna da dama amma abinda yafi muhammanci shine kasancewarshi jigo kuma manuniya a harkar kwallon kafa ga miliyoyin mutane. Tace Ronaldon bashi da wanda za'a gwadashi dashi.

A karshe ta bayyana cewa shine na daya kuma tana sonshi jaridar abokin aikinmu hutudole ya ruwaito wannan labari.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: