Sunday, 1 December 2019
Ina Da Tabbacin Mutane Da Yawa sun Shiryu Saboda Kallon Fina Finanmu - Teema Makamashi

Home Ina Da Tabbacin Mutane Da Yawa sun Shiryu Saboda Kallon Fina Finanmu - Teema Makamashi
Ku Tura A Social Media
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Teema Makamashi ta bayyana cewa ta san mutane da dama masu aikata laifukan sata da karuwanci da suka shiryu ta dalilin kallon fina-finan Hausa.

Jaruma Teema Makamashi ta bayyana hakan ne a yayin da take zantawa da gidan Rediyon Dala, inda tace babban aikinsu shi ne gyaran tarbiyyar al’umma, sai dai kawai wasu bata gari na bata musu suna, wajen aikata wasu munanan dabi’u da sunan ‘yan film.

Jarumar ta musanta rade-radin da ake yadawa a gari na cewa jaruman masana’antar Kannywood basu da tarbiyya, sannan tayi kira ga ‘yan uwanta jarumai na masana’antar da su maida hankali wajen cigaban masana’antar maimakon fadace-fadace a tsakanin su.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: