Kannywood

Fina-finan Kannywood 10 da suka fi shahara a 2019

Muhsin Ibrahim, Malamin harshen Hausa ne a jami’ar Cologne da ke Jamus kuma Malami a sashen nazarin wasannin kwaikwayo a Jami’ar Bayero ta Kano

DagaMuhsin IbrahimJami’ar Colonge
Har yanzu dai masana’antar fim din Hausa, wato Kannywood, tana nan daram. Kamar yadda watakila mutane da yawa suka sani, masana’antar tana fama da kalubale iri-iri.
Lokaci zuwa lokaci, takan samu kanta cikin abubuwa da babu dadin ji. Mafiya shahara daga abubuwan a wannan shekarar su ne, yadda siyasa ta kawo rabuwar kai a tsakanin ‘yan masana’antar.
Sannan, wasu jarumai mata sun samu rashin jituwa har ya kai ga bidiyon rikicin nasu ya karade ko’ina; da kuma kama wani shahararren mai ba da umarni; sannan da yadda yanayin suturar wasu jarumai mata ya janyo wa masana’antar Allah-wadai da zagi da tsinuwa, da dai sauran abubuwa.
Zan iya cewa ban kalli wasu fina-finai da ya kamata su zama suna cikin shahararru 10 na shekarar 2019 ba.
To sai dai ba a Kano nake ba, ta yadda zan rika zuwa sinimar Kano guda dayar nan, inda a nan ne ake gabatar da fina-finan Kannywood ga jama’a.
Saboda haka, wadannan suna cikin fina-finan da suka kece raini a cikin shekarar nan. Sannan, ba bisa daraja aka jero su ba.
1. Doya da Manja

Doya da ManjaHakkin mallakar hotoOFFICIAL KANNYWOOD

Shi wannan fim din babu kamarsa a Kannywood. Ya hado kan Hausawa da Yarabawa ne, biyu daga cikin manyan kabilun Najeriya uku, ta hanyar mu’amala da auratayya.
Hafsat Idris ce, a matsayinta na Bayerabiya a fim din, ta fara soyayya da Aminu Sharif Momoh, Bahaushen dan sanda, wanda ya ceceta daga hannun wasu ‘yan iska.
Dukkansu biyun sun fuskanci kalubale daga wajen ‘yan uwa da iyayensu saboda bambancin kabilar da ke tsakaninsu. Sai dai daga bayan sun shawo kan duka matsalolin, sannan suka yi aurensu kuma suka rayu cikin farin ciki.
Wannan fim ya cancanci jinjina saboda irin yadda sautinsa ya fito ral da yadda kowane jarumi ya yi matukar abin da ya kamata, musamman yadda Hafsat Idris ta kwalmada muryarta ta koma kamar ba ta Hausawa ba.
Jigon fim din ma ya bayar da ma’ana ganin yadda ya yi kokarin hado kan wadannan kabilun. Sai dai, duk da haka, fim din ya yi tsawo da sauran ‘yan matsaloli dai nan da can.
2. Hauwa Kulu

Hauwa KuluHakkin mallakar hotoABBA MAISHADDA

Wannan shi kuma yana bayar da labarin wata da aka taba yi mata fyade ne, wacce ta girma ta zama alkali da ba ta lamuntar rashin gaskiya.
Sai dai an taba kawo mata karar wani al’amari da ya tayar mata da tsohon miki har ma ya kusa saka ta yin rashin gaskiya. Hajara Usman ita ta ceci Hauwa Kulu kuma ta tallafa mata wajen gina rayuwarta bayan da mai garinsu, mai matukar son mata ya lalata ta.
Daga baya sai ta (wato Hajara Usman) hada su aure da danta, Ali Nuhu, wanda har suka haifi yaro daya. Wannan yaron shi ne ya yi fyade wa ‘yar aikin gidansu, har aka kai al’amarin gaban kotun Hauwa.
Fim din ya dace da wannan zamanin sannan yana dauke da abubuwan jarumta. Zai yi tasiri ga wadanda suka kalle shi. Na jinjina wa fim din sosai saboda irin jigonsa da yanayin tsarinsa da yadda jaruman suka tafiyar da shi.
Sai dai, da zai fi idan da an sauya wasu abubuwa: yadda aka sanya Gabon — budurwa da ita — ta zama mahifiya ga saurayin da ya riga ya girma; da bukatarta ta neman hakki a matsayinta na wadda aka yi wa fyade; da sauransu.
Ali Nuhu ne daraktan fim din yayin da Bashir Maishadda kuma shi ne furodusa.
3. Tsalle Daya

Tsalle DayaHakkin mallakar hotoINSTAGRAM

A hankali dai, masu shirya fim a Kannywood suna dagewa wajen zabar abun da za su yi fim a kai. Tsalle Daya wani shiri ne game da yadda satar mutane don kudin fansa ya yawaita a Najeriya.
Wasu lokuta, mutane sukan yi karyar an sace su, ko ‘yan uwansu don samun kudi wajen wani. A wannan shirin, Jamila Nagudu ce ta kitsa makircin satar danta don ta samu kudi a wajen mijinta, Ali Nuhu.
Lokacin da ‘yan sanda suka yi bincike sai suka bankado wasu boyayyun al’amura masu tayar da hankali. Daga karshe dai a haka dan nan natan ba a samu
an kubutar da shi ba.
Fim din ya dace da wannan lokacin, kuma yin irinsa ba karamar jarumta ba ce. Nagudu da Teema Yola da Daso, da sauransu sun taka rawar gani. Duk da cewa wakar ciki ta kayatar, amma babu bukatarta sosai.
4. Yanayi

YanayiHakkin mallakar hotoSUNUSI OSCAR

Wannan kuma labarin wata harija ce, Hajiya Sha’afatu (Zainab Indomie), wacce mijinta dattijo ne, ya rasa rayuwarsa a kokarinsa na biya mata bukata irin ta aure.
Bayan mutuwar tasa sai ta koma mai biye-biyen samari don yin lalata (abin da a Turance a ke cewa “Sugar Mummy”).
Sai take ta yaudarar samari don samun biyan bukatar sha’awarta — ciki har da dan uwan kawarta da kuma saurayin da ‘yarta za ta aura. Daga karshe dai al’amura suka juya mata baya.
Fim din yana koyar da darussa ta hanyar gargadi daga fadawa harkar biye-biye ta “Sugar Mummy.”
A ƙoƙarin fim din na fayyace komai game da irin wannan harka, sai kuma aka so a dan kauce hanya. In da an saye wasu al’amura, da abin ya fi kyau.
Sunusi Oscar 442 ne daraktan, sannan Naziru Dan Hajiya kuma shi ne furodusa.
5. Namijin Kishi

Namijin KishiHakkin mallakar hotoYAKUBU KUMO

Wannan fim labari yake bayarwa a kan Habibu (Sadiq Sani Sadiq) mutum mai matukar kishi, wanda kullum kokarinsa shi ne ba da kariya wa kyakkyawuyar matar nan tasa, Fa’iza (Hafsat Idris), daga shiga hurumin kowane mutum idan ba shi ba.
Aurensu bai yi tsawo ba saboda ya sake ta. To sai dai Habibu yana son Fa’iza matuka, har ya yi kusan haukacewa saboda bukatarsa ta sake aurenta – abin da ba mai yiwuwa ba ne.
Da hakan ya ki yiwuwa, sai ya fara kokarin hana ta sake aure. A karshe dai ya fahimci kuskurensa kuma ya yi nadama.
Daraktan fim din, Ali Gumzak, tare da furodusan, Yakubu M. Kumo, sun yi kokari. Fim ne na ban-dariya mai dauke da jigo da zai iya ba da tausayi.
Wannan shi ne dalilin da ya sa mutum zai iya shiga bakin cikin idan yana kallonsa. Ba makawa, duk da bajintar Sadiq Sani Sadiq, ya dan so ya wuce misali a wasu wuraren.
Sannan, da ya kamata a tafiyar da wasu abubuwan a kan doron bincike da ilimi saboda muhimmancinsu ga aure da kuma mahangar Addinin Musulunci, musamman a arewacin Najeriya – inda nan ne mutuwar aure ta yawaita.
6. Jidda

JiddaHakkin mallakar hotoALI GUMZAK

Shi kuma wannan labarin wasu kawaye ‘yan makaranta biyu ne, Salma da Jidda. Yayin da ita Salma ta fito ne daga gidan masu akwai, Jidda kuma ba su da karfi.
Wata rana sai suka samu rashin jituwa, har Jidda ta sha alwashin kashe Salma. Washegari kuwa sai aka samu gawar Jidda.
‘Yan sanda kuwa sai suka kama Jidda – da zargin aikata kisan. Aka same ta da laifi har aka yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Daga baya kuwa, saurayinta, wanda lauya ne (Ibrahim Maishinku), ya zurfafa bincike sai ya gano ashe kawunta ne ya kashe ta – wanda ta kama shi yana kwanciya da mahaifiyarta duk lokacin da mahaifinta ba ya nan.
Yayin da Ali Gumzak ne darakta, Alhaji Sheshe kuma furodusa, Jidda ya samu jinjina ne saboda dalilai da dama. Ya kayatar, kuma ya sanya wa masu kallo son ganin me zai faru a gaba ne saboda sai a karshe ne kowace matsala ta warware.
Abin ya kayatar ganin yadda aka tsara fim din da yanayin kwalliya da kuma yadda kowane tauraro ya taka rawar gani. Sai dai an samu maimaicin wasu wurare da hirarraki.
7. Manyan Gobe

Manyan GobeHakkin mallakar hotoALI GUMZAK

Shi wannan shirin fim ne na daban. Labari ne a kan cutar shan-inna. Wani mutum ne da bai yi wani karatu ba (wato Al-Amin Buhari), wanda a kullum shi adawa yake yi da duk wani abu na zamani – ciki har da riga-kafin shan-inna.
Sannan ya hana matarsa (Jamila Nagudu) shan duk wani magani (ko na tsara iyali). Shi cewa ya yi ma duk wani abu mai kama da wannan ya saba wa Musulunci. Daga karshe dan daya ya mutu; dayar ‘yar tasu Maryam kuma shan-inna ya gurgunta mata duka kafafuwanta.
Bayan haka kuma ya saki matarsa, sai al’amura suka kara rincabewa. Ta dalilin kungiyar tallafi ta Muhammadu Sunusi, gurguwar ‘yar nan tasu ta samu damar nuna bajintarta a fagen ilimi.
Muhammad Nata’ala shi ne furodusan, Ali Gumzak kuma darakta. Fim din ya tabo al’amura ne game da mu’amala da al’ada kan yadda ake da kuskuren fahimta game da riga-kafin shan-inna.
Kuma yana assasa wanzuwar limi — musamman na ‘ya mace — wanda yawancin iyaye suke masa riƙon sakainar kashi.
8. Madubin Gobe

Madubin GobeHakkin mallakar hotoSULAIMAN BELLO EASY

Wannan, kamar sauran fina-finai, kagaggen labari ne amma cike yake da darussa. Ibrahim Mandawari, wani hamshakin mai kudi, wata rana kawai sai ya bayyana wa iyalinsa cewa duk abubuwan nan da ya mallaka fa ba nasa ba ne.
Ya mayar da duk abubuwan da ya mallaka, ciki har da gidansa, ga wani talakan da ba a ma san shi ba (wanda Shehu Hassan Kano ya fito a matsayinsa). Haka dai ya koma gidan laka a kauye.
Bayan haka ya faru, sai abubuwa suka sauya: Shehun da a baya mataulauci ne kawai sai shi da matarsa suka fara wulaƙanci, rashin gaskiya, almubazzaranci, da sauransu.
Mai ba su tallafin sai ya yi amfani da wani ma’aikancinsa don ya jarraba su — ba su samu nasarar cin jarabawar nan ba kuwa. Saboda haka sai ya dawo ya karbe dukiyarsa.
Daraktan Sulaiman Bello Easy ne. Furodusa kuma Kabiru A. Yako. Shirin fim din ya cancanci jinjina saboda nuninsa ga yadda dan’adam yake da mantuwa da mugunta.
Wannan ya dace da fadin Hausawa: “Allah ya san halin jaki da bai yi shi da kaho ba”. Sai dai shirin ya yi tsayi, kuma wasu jarumai ba su yi wani abin-a-zo-gani ba.
9. Dawood

DawoodHakkin mallakar hotoSUNUSI OSCAR

Kamar yadda sunan ya nuna, fim din ya ta’allaka ne a kan Dawood (Ali Nuhu), wani mutum mai kudi da kuma karamci cikin al’ummar da yake.
Yana da ‘ya, Balkisu Shema, wacce k
awarta kuma ‘yar ajinsu, Rahama Nijar, ta tsinci kanta cikin matsi na rashin kudi. Yana jin haka a wajen ‘yar nan tasa, sai ya kawo mata agaji.
Ya biya wa Rahama kudin makaranta, kuma ya taimaka wa iyayenta. Hakan sai ya sa ya samu farin jini a wajen Rahama. Lokacin da aka ce ta fito da miji, kawai sai ta ambaci Dawood.
Matarsa, marigayiya Hauwa Maina da diyarta suka dai karbe ta hannu bibbiyu a matsayin abokiyar zama. Kamar dai yadda karin maganar ke cewa, “babu abin da ya kai karamci saka mutum samun farin jini.”
Fim din, wanda Abdulaziz Dansmall ne furodusa, Sunusi Oscar kuma darakta, ya yi kokarin gasgata waccar karin maganar.
Labarin gajere ne kuma watakila za mu iya cewa bai yi kama da abin da zai faru a zahiri ba. Baya ga haka, duk ‘yan wasan sun taka rawar gani.
10. Barazana

BarazanaHakkin mallakar hotoTJ SHABAN

Wannan shiri, wanda ya samu lambobin yabo iri-iri, an yi shi ne a kan “fashi da makami,” da “satar mutane,” da kuma yunkurin ‘yan sandan Najeriya wajen ganin masu irin wadannan laifuka sun fuskanci fushin doka.
A bayyane yake cewa ‘yan sandan Najeriyar sun tallafa wa masu yin fim din wajen shirya shi.
Amfani da gine-gine da motoci da inifom da wasu abubuwa na ‘yan sandan abu ne da ya kayatar, kuma za a iya cewa ba a taba ganin irin hakan ba.
Shirin fim din ya yi zarra gami da samun kimtsattsen tsari kuma mai jan hankali. Daya daga cikin manyan jaruman fim din, TY Shaba, shi ne furodusa, Muhammad Bashir Waya kuma shi ne darakta.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button