Kannywood

Babu Maganar Aure Tsakanina Da Kamaye – Jaruma Adama Ta Dadin kowa

Duk A Cikin Shirin ‘Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuraɗiyya Ke Ɗaukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Ga duk wanda ya ke kallon shirin Dadin Kowa na Arewa 24 ya san Adama wato Hajiya Zahra’u matar Kamaye, wato Dan’azumi Baba, Cediyar ‘Yan Gurasa, da kuma irin zaman da su ke na rikici, a zaman su na miji da mata.

Sai dai duk da haka, mutane su na yi musu kallon wadanda su ka dace da zaman aure a zahiri, wannan ce ma tasa ake ta yada jita jitar za su yi aure  tsakanin su.

Ganin yadda maganar a yanzu ta ke ci gaba da yaduwa ne ya sa mu ka nemi jin ta bakin su, sai dai ba mu samu ji daga Bakin Kamaye ba, Amma dai mun samu zantawa da Adama, kuma ta yi wa wakilin mu mukhtar yakubu, bayani dangane da alakar su da Kamaye da kuma yadda ta ke kallon sa, in da ta fara da cewa.

To gaskiyar magana auren mu da Dan’azumi Baba, wato Kamaye, ni ma dai abin da naji ana fada kenan amma dai tsakanina da shi babu wata maganar aure, domin ko Soyayya ma ba ta shiga tsakanin mu ba, kawai dai mutane ne su ke yanke mana hukunci'”

Mun tambaye ta Ko ba kya ganin irin yadda ku ke zaman aure a cikin shirin Dadin Kowa ne ya sa ake wannan maganar?

” To ai wannan ana ganin Kamaye ne da Adama Amma a zahiri Dan’azumi Baba ne da Hajiya Zahra’u don haka mutane su gane shiri daban, rayuwa ta zahiri daban, domin ni ina daukar Dan’azumi Baba ne a matsayin Yaya na, kuma uban gida na a harkar fim saboda haka mutane su daina kallon mu ma a matsayin masoya, ni kanwar sa ce, kuma uban gidana ne”.

Dangane da harkar fim ko Hajiya Zahra’u ta cimma burin ta?

“To gaskiya zan iya cewa na cimma buri na, domin na samu arzikin jama’a, a yau ba a nan kasar ba duk duniya ina da masoya, kuma ina yin alfahari da su, don haka babu abin da zan ce sai dai godiya ga Allah, kuma ina kira ga ‘yan baya da su gane cewa daukaka ta Allah ce kada mutum ya rinka tunanin shi sai ya daukaka, mu da mu ka shigo harkar ba mu zata Allah zai kaimu ga wannan matsayin ba, don haka mutane a rinka yin tawakkali ana mika lamari ga Allah, inji Adama.

Haƙƙin Mallaka, Jaridar Dimokuraɗiyya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button