Kannywood

Ba wai Rawa Da waka Ne ke Da muhimmanci a fim Ba – Zulaihat ZPreety

– Zulaihat Ibraheem jaruma ce da aka fi sani da ZPreety bata dade da shigowa masana’antar Kannywood ba amma ta samu daukaka mai tarin yawa,

– An haifeta ne a 1997 kuma ‘yar asalin jihar Kebbi ce daga kauyen Rubba dake karamar hukumar Dankuwa

– Jarumar ta bayyana cewa, ta shigo harkar fim amma hankalinta na kan aure, a duk lokacin da ta samu miji zata bar fim ta yi aurenta

Zulaihat Ibraheem jaruma ce da aka fi sani da ZPreety. Jaruma ce da bata dade da shigowa masana’antar Kannywood ba amma ta samu daukaka mai tarin yawa. Ba a fim kadai ta tsaya ba, ta kasance tana yin gajerun bidiyon ban dariya inda take wallafa su a shafinta na Instagram. Hakan kuwa ya sa tayi farin jini da karin suna.

Kamar yadda jarumar ta bayyanawa jaridar Fim Magazine, an haifeta ne a 1997 kuma ‘yar asalin jihar Kebbi ce daga kauyen Rubba dake karamar hukumar Dankuwa. Don haka asalin iyayenta Dakarkari ne a yankin Zuru.

Kamar yadda ta bayyana, tayi karatun firamare a barikin sojoji na jihar Legas saboda mahaifinta ma’aikacin hukumar kula da shige da fice ne wato Nigerian Immigration Service. Ta yi sakandire a Kontagora a jihar Neja. Tayi karatu a kwalejin horar da malamai ta tarayya da ke Sokoto amma a halin yanzu tana jami’ar ABU Zaria inda ta ke matakin kusa da na karshe na kammala digirinta na farko.

Bayan da wakilin jaridar ya tambayeta yadda ta fada harkar fim bayan kuma malama ce, sai ta ce, “Tun ina karama nake da burin tallace-tallace. Amma da na girma sai na gane cewa ba zan samu cikar buri na ba, ba tare da na yi suna ba. Hanyar da zanyi suna kuwa itace in fada harkar fim. A 2017 na shigo kuma Alhamdulillahi yanzu na yi fina-finai sama da 20.”

A lokacin da aka tambayeta ko dama ta iya rawa kafin shigowarta masana’antar ganin ta gwanance a rawa da waka, sai ta bayyana cewa, “To ni ina ganin rawa wata halitta ce da ko mutum bai je makaranta ba zai iya, domin kuwa yanayin rawa a jiki ya ke; ka na zaune za ka yi, kuma ka na tsaye ma za ka yi. Don haka a yanayi na ina ganin zan iya yin kowace irin rawa.”

Jarumar ta bayyana cewa, ta shigo harkar fim amma hankalinta na kan aure, a duk lokacin da ta samu miji zata bar fim ta yi aurenta. Domin kuwa aure sunnar annabi ce kuma ta hanyarshi aka samemu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button