Sunday, 22 December 2019
Aljanar duniya: Hotunan cikin katafaren Gidan Attajiri, Aliko Dangote

Home Aljanar duniya: Hotunan cikin katafaren Gidan Attajiri, Aliko Dangote
Ku Tura A Social Media
Aliko Dangote shine bakin mutum mafi kudi a duniya a yau. Ba abun mamaki bane idan aka ce yana rayuwa a gidan da za a kira da 'aljannar duniya'. Rade-radi sun bayyana cewa, gidan Aliko Dangote ya kai darajar $30million. Gidan na nan a Abuja. Zata yuwu gidan ne gida mafi kyau da mai karatu ya taba gani.

A ta wajen gidan, anyi masa fenti da farin gilashi inda aka yi masa yarfi a jiki duk da tagogin. Katangar gidan da ke zagaye da daular duniyar itama tana da fenti fari ne. Kofar gidan wani katon bakin get ne wanda ya tsaru saboda farin fenti dake kewaye da gidan. Harabar gidan kuwa a tsaftace take a koda yaushe kuma ta kawatu da ciyawa launin kore.Gidan Aliko Dangote ta gaba
A ta cikin gidan kuwa, an tsara ne da wasu irin kayan kawa na 'Victorian Beauty'. A takaice dai, kowanne daki dake cikin gidan nan ya tsaru. Akwai katon daki wanda aka kawata shi da manyan kujeru da kuma wasu irin kayan haske tare da fenti mai matukar kawatar da wanda ke kallo.


Gidan Aliko Dangote

Kamar yadda rade-radi ke nunawa, wannan shine dakin da Dangote ke amfani dashi matukar zai yi taronsa na kasuwanci ko wata tattaunawa da jami'an gwamnati ko abokan kasuwanci.

Madafin gidan kuwa, wani abun kallo ne na daban kamar a aljanna. Haske da yanayin tsarin madafin kuwa, ba abu ne da mai karatu zai iya kintatawa ba. Da yawa daga cikin otal din Najeriya, ba a samun kamarsa.


Kitchen

Akwai wani katon talabijin da ke sagale a daya daga cikin ginshikan madafin. Wajen ajiye-ajiye na madafin kuwa duniya ce ta daban. Akwai kujerun da mutum zai iya zama a kusa dasu.

Dakunan baccin wannan gida kuwa ba abu ne da mai karatu zai iya fahimta ba matukar bai ga hoton ba ko kuma ya je da kansa.


Dakin bacci

Share this


Author: verified_user

0 Comments: