Thursday, 12 December 2019
Adam A Zango ya zama jarumin farko da kamfanin YouTube Ya karrama Da kambun azurfa

Home Adam A Zango ya zama jarumin farko da kamfanin YouTube Ya karrama Da kambun azurfa
Ku Tura A Social Media
- Kamfanin YouTube na kasar Amurka ya karrama fitaccen jarumin fina-finan Hausa Adam A Zango

- Kamfanin ya bawa jarumin kyautar wani kambu na azurfa, bayan ya samu adadain mabiya dubu dari a shafinsa na YouTube

- Wannan kyauta ita ce ta sanya jarumin ya zama na farko a cikin jarumin Kannywood da kamfanin YouTube ya bawa irin wannan kyauta

Sanannen jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, Adam A Zango wanda a kwanakin baya ya bayyana cewa ya bar masana'antar ta Kannywood saboda wasu dalilai.


Adam A Zango ya zama jarumin farko da kamfanin YouTube ya karrama da kambun azurfa

A wannan karon dai kamfanin YouTube ne dake kasar Amurka ya karramashi da wata gagaruwar kyauta.

Kamfanin ya bawa jarumin kyautar wani kambu na azurfa, sakamakon cika adadin mabiya dubu dari da yayi a shafin nasa na YouTube.

Jarumin ya samu wannan kyauta ne saboda yawan sanya wakoki, fina-finai, wasanni da kuma hirarraki da yake yi a shafin nasa.

Jarumin ya wallafa hotonsa a shafinsa na Instagram rike da kyautar da aka aiko masa tun daga kasar Amurka.

Haka zalika a kasan hoton jarumin ya rubuta sakon godiya ga kamfanin na YouTube da kuma daukacin masoyansa da suka bada gudummawa wajen ganin ya samu wannan nasara.


Wannan kyauta da jarumin ya samu dai ita ce ta sa ya zama jarumi na farko a masana'antar Kannywood da ya samu irin wannan kyauta.

A karshe dai muna taya jarumin murnar wannan gagarumar nasara da yayi, sannan kuma muna taya sauran jarumai da al'umma Allah ya cigaba da daukaka lamuran su na yau da kullum domin ganin sun cimma nasara akan dukkan abinda suka sanya a gaba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: