Monday, 30 December 2019
A kakkafa Mana sinimomin Nuna fim ɗin Hausa –Haruna Talle Maifata

Home A kakkafa Mana sinimomin Nuna fim ɗin Hausa –Haruna Talle Maifata
Ku Tura A Social Media
Haruna Telle Maifata da ke zaune a garin Jos, mai shiryawa da bada umarni da daukar nauyi da kuma rubuta fina-finan Hausa ne. Kuma shi ne Shugaban Kamfanin Maifata Pictures Nigeria Limited, wanda zuwa yanzu, ya shirya fim din Hausa sama da 50.  A tattaunawa wakilinmu, ya ce babban kalubalen da masu shirya fina-finan Hausa suke fuskanta a yanzu shi ne harkokin wayar hannu:Ku masu shirya fina-finan Hausa wane kalubale ne kuke fuskanta a yanzu?

Gaskiya halin da muke ciki yanzu  hali ne na kaka-ni-ka-yi. Dalili kuwa shi ne yanzu harkokin fina-finai na duniya ya yi gabas, mu kuma masu fina-finan Hausa mun yi yamma. Abin da ya sa na ce haka, yanzu a duniya ba a maganar DBD ko CD, ko a nan kasashen Afirka idan ka je wata kasar, kana maganar DBD ko CD dariya za a yi maka, saboda an wuce wannan waje.Yanzu duniya ta dawo tafin hannu ta hanyar waya. Mutum ta hanyar wayar hannunsa zai iya sanin me ake yi a kowace kasa a duniya. Abin da yake faruwa kuma mu masu fina-finan Hausa a da muna amfani da bidiyo ne, daga nan aka dawo DBD daga nan aka dawo BCD, har yanzu  muna nan a BCD. Kuma matsalar da aka samu, yanzu ita ce an bar BCD an koma wayoyin hannu.

Yanzu idan ka je kauyuka za ka ga wayoyi a hannun mutane suna dauke da fina-finan Hausa. Shi mai fim da ake tura fina-finansa a wadannan wayoyi ba ya karuwa da komai. Za ka ga mai fim ya kashe Naira miliyan hudu zuwa biyar, sai mai shago ya sa yi kaset din fim na Naira 200 ya rika tura wa mutane kan Naira 20, mutum daya kuma ya tura wa kamar mutum 100 kyauta, a wayoyinsu. Ka ga mai fim ya tashi a banza ke nan.

Muna yin fim din nan, kuma muna kawo ayyukan yi ga matasan kasar nan. A kullum ’yan siyasa suna daukar ’yan fim suna tallata su, don haka ya kamata in sun kafa gwamnati su rika yi mana abubuwan da za mu samu ci gaba. Amma idan suka hau mulki suna mantawa da mu.

A shekara uku da suka gabata babu yadda mutum zai yi fim ya ce ya yi asara, amma sakamakon wannan hali da muke ciki yanzu, babu yadda mutum zai shirya fim ya samu riba.

Yanzu ina da fina-finai da na shirya sun fi 10. Kwanakin baya na hau jirgi na je Legas na zauna da Kamfanin Gidan Talabijin na DSTB suka sayi  fina-finan, sai na ga kudin da suka sayi  fina-finan ba su kai kudin da na kashe ba. Kuma tunda suka saya, har yanzu ba su biya ni ba. Bayan haka akwai wani kamfanin Intanet da ke YouTube mai suna, NorhtFlid nan ma suka karbi fina-finaina suka ce za su rika sanyawa, ana turawa a wayoyi.  A duniya duk mutumin da aka tura wa fim kan Naira 200, su suna da Naira 40, mai fim yana da Naira 20, su ma har yanzu suna nan suna ce mana suna shirye-shirye na fara biyanmu amma har yanzu, ba su fara biyanmu ba, duk da suna saka fina-finanmu.Da wannan dalili nake kalubalantar gwamnati cewa da take yi za a ba mu rancen kudi, ba rancen kudi ya kamata a bai wa masu shirya fina-finan Hausa ba, a gina mana gidajen nuna fina-finai a kasar nan muke bukata.

Wato a ganinka gina gidajen nuna fina-finai ne mafita kan halin da kuke ciki?

Babu shakka gina gidajen nuna fina-finai ne mafita. Domin yanzu misali idan ka je kasar Indiya, akwai manya-manyan gidajen nuna fina-finai da aka gina. Kuma ake nuna fim daya a rana daya a dukkan wadannan gidajen fim da ke garuruwa daban-daban. Idan aka yi irin wadannan gidajen nuna fim a Najeriya, aka nuna fim daya a rana daya, sai ka ga mai fim ya hada kudin fim din da ya yi a rana daya.

Idan aka gina mana gidajen nuna fina-finai muna nuna fim dinmu, kuma aka samar mana da yadda da za a rika tura fina-finanmu babu wata matsala.

Ko kungiyarku ta taba yin wani yunkuri na magance wannan matsala?

Babu irin yunkurin da ba mu yi ba. Mun je mun zauna da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kuma ya yi mana alkawarin cewa za a ba mu rancen kudi. To amma ni yanzu ba na cikin wadanda za su karbi wannan rance, saboda ba na son abin da zai zo ya dame ni. Idan da an ba ni rancen kudi ne na shirya wadancen fina-finai sama da 10 da na ba ka labari da ba zan zauna lafiya ba. Don hak

Share this


Author: verified_user

0 Comments: