Saturday, 9 November 2019
Zuwan 'Yan Fim A Birnin Landan Akwai Wakilcin Hausa Kuwa ?

Home Zuwan 'Yan Fim A Birnin Landan Akwai Wakilcin Hausa Kuwa ?
Ku Tura A Social Media


Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

A karshan satin da ya gaba ta ne wasu daga cikin' yan fim wato Fati Washa, Rahama Sadau, Hadiza Gabon suka halarci bikin karrama 'yan fim da ake gudanarwa duk shekara, in da kuma a wannan shekarar suna daga cikin' yan fim da aka karrama a cikin masana'antar finafinai ta kannywood.

Tun daga lokacin da aka gudanar da gasar har zuwa yanzu hotunan jaruman ne suka cika duniya tun daga wajen da aka karrama su da kuma wuraren da suka halarta domin yawon shakatawa,.

Hotuna ne dai ga su nan barkatar ana yadawa da sunan 'yan fim din hausa a birnin Landan ko ina zuwa suke suna daukar hotuna, amma dai daga yadda jaruman suka rinka yin shiga a hotunan na su babu wata alama da ta nuna wakilcin fim din hausa ko kuma finafinan Hausa, domin kuwa babu wata shiga ta kasar hausa da jaruman suka yi wadda za ta nuna daga kasar hausa suke kuma darajar fim din hausa ce ta sa suka samu kan su a wata duniya mai nisa.

Don haka dai magana ta gaskiya babu wani alfahari da Bahaushe zai yi da wakilcin da su Fati Washa, Rahama Sadau, da Hadiza Gabon, suka yi masa.

Hakan ce ta sa mutane da dama da suke da kishin hausa da kuma al'adun hausa suka yi ta Allah wadai da irin wannan wakilci da wadanan jaruman suka yi wa Harshen hausa a birnin Landan.

Me za Ku Ce?

Share this


Author: verified_user

0 Comments: