Monday, 11 November 2019
Zargin Madigo : Kotu Ta Kori Karar Hadiza Gabon Da Amina Amal

Home Zargin Madigo : Kotu Ta Kori Karar Hadiza Gabon Da Amina Amal
Ku Tura A Social Media
Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Babbar kotun tarayya mai lamba 2 dake Kano wadda mai Shari'a O, A, Oguata ya ke jagoranta, a shekaran jiya juma'a, ta kori karar da Amina Amal ta shigar a gaban ta in da take neman kotun ta bi mata hakkin ta a wajen Hadiza Gabon saboda bata mata suna da ta yi.

Tun a watan Afrilun da ya gabata ne dai Amina Amal ta shigar da karar in da Amal take bukatar kotun da ta Sanya Hadiza Gabon ta yi Abu hudu wadanda suka hada da ta bata hakuri a rubuce, kuma a wallafa bada hakurin a shafukan manyan jaridu na kasar nan, guda biyu, kuma kotu ta hana ta ko wani nata ci mata mutunci, sannan kuma ta biya ta diyyar Naira miliyan 50 saboda bata mata suna da ta yi.

Kuma lauyoyi 15 ne suka saka hannu a takardar a wancan lokacin ta Chambar A A Umar (SAN) dake unguwar farm center a Kano.

Bayan tsawon watanni da aka shafe ana shari'ar a yanzu dai alkali ya kori karar a sakamakon rashin gamsassun hujjoji da Amina Amal ta yi wajen shigar da karar, don haka ne a zaman kotun na ranar juma'a 8 ga watan Nuwamba ta kori karar, Wanda Hakan ya kawo karshan wannan Shari'ar.

Sai dai abin jira a gani shi ne, ko Amina za ta daukaka Kara, ko kuma za ta hakura haka?

Domin duk wani kokari na jin ta bakin ta ko wani daga cikin lauyoyin ta abin ya ci tura.

Share this


Author: verified_user

1 comment: