Thursday, 7 November 2019
Zaku iya auren 'ya'yan da ku ka haifa ba ta hanyar aure ba - Babban Malamin Islama

Home Zaku iya auren 'ya'yan da ku ka haifa ba ta hanyar aure ba - Babban Malamin Islama
Ku Tura A Social Media
Shafinmu ya samu wannan bayyani daga shafin Dokin Karfe a facebook.

Shahararren Malamin addinin Islama da yake koyarwa a Jami'ar Al-Azhar dake kasar Egypt ya bayar da fatawar cewar ya halasta ga maza su sadu da 'ya'yan su mata har ma su aure su, matukar ba ta hanyar aure suka haifi'ya'yan ba.

Wani fitaccen malamin Salafiyya a kasar Egypt, Mazen Al-Sersawi, ya sanar a cikin wa'azin sa cewar maza na iya saduwa da 'ya'yan su mata har ma su iya yin aure matukar ba ta hanyar aure suka haifi 'ya'yan ba.

Wata jarida, Daily Mail UK, ta wallafa cewar Al-Sersawi ya kafa hujja da fitaccen malamin islama Imam Al-Shafi'i yana mai bayyana cewar addini musulunci bai alakanta 'ya'yan da aka haifa ba ta hanyar aure ba da iyayensu ba, a saboda haka iyayen na iya auren su.

Malamin addinai dai ya sha suka biyo bayan bayar da wannan fatawa.

Al-Sersawi yana koyarwa ne a jami'ar Al-Azhar ta kasar Egypt, kuma ya bayyana cewar "'yar da mutum ya haifa ta hanyar zina ba cikakkiyar 'ya ba ce domin ko a shari'an ce na zata yi lakabi da sunan uban nata ba, a don haka aure tsakanin ta da mahifin nata ya halasta".

Wani Malamin addinin Islama a kasar ta Egypt, Muftah Mohammad Maarouf, a farkon shekarar nan, yayin wata mahawara a gidan talabijin ya bayyana cewar mutum kan iya auren jaririya, a kokarin sa na kare aurar da 'ya'ya mata ma su karancin shekaru.

Ya bayyana cewar "babu haramci ga auren mace duk karancin shekarar ta matukar ba za a cutar da ita ba domin a addinin musulunci ba a kayyade shekarar da za a aurar da 'ya mace ba".

Share this


Author: verified_user

2 comments: