Wednesday, 6 November 2019
Za mu Yi kokarin dawo Da kimar masana`antar Fim- Dakta Ahmad Sarari

Home Za mu Yi kokarin dawo Da kimar masana`antar Fim- Dakta Ahmad Sarari
Ku Tura A Social Media
Shafin Northflix ya wallafa,Sabon shugaban kungiyar kwararru ta masu shirya fim ta kasa MOPPAN Dakta Ahmad Sarari ya bayyana kokarin sa na dukufa wajen dawo da kima da kuma darajar masana'antar Kannywood a idon duniya a lokacin gudanar da mulkin sa.

Dakta Ahmad Sarari ya bayyana hakan ne a lokacin da su ke tattaunawa da wakilin mu a game da nasarar da ya samu a lokacin da aka gudanar da zaben makonni biyu da suka gabata.

Tun a farkon tattaunawar ya nuna godiyar sa ga Allah ga kuma 'yan kungiyar bisa zaben sa da suka yi, kuma ya yi alkawarin ba zai ba su kunya ba domin haka ya ke neman goyon bayan su don ya samu damar sauke nauyin da ya ke kan sa.

Ya kara da cewa “masana'antar fim a yanzu tana cikin wani yanayi na mutuwar kasuwancin fim domin haka ne mu ke son bullo da dabaru na kasuwancin fim kamar yadda sauran kasashe suke kokarin zamanantar da harkokin kasuwancin fim yadda ya ke tafiya da zamani, don haka ni daman Ina da tsarin da na shigo da shi na yadda ake sana'ar fim a duniya sai mu duba mu ga ta ina za mu fara, amma dai mutane su sani kasuwancin fim tun tuni ya tashi daga kasuwar kofar wambai ya koma harka ta duniya gaba daya, don haka ya zama dole masu gudanar da harkar fim su koyi tafiya da zamani, Mu dai kudurorin da muke shine na kawo gyara a cikin  harkar fim kuma za mu tsaya tsaiwar daka domin cimma wannan kudiri, muna fatan Allah ya ba mu damar sauke nauyin da ya ke kan mu”.

Ya kamala da cewa, gyaran harkar fim ba abu ne na mutum daya ba don haka ya na neman gudummawar kowa da kowa”. In ji Dr. sararin

Share this


Author: verified_user

0 Comments: