Tuesday, 19 November 2019
YARIMAN BAKURA YA FASA KWAI YACE :~ Buhari Ne Ya Nemi A soke zaben Zamfara

Home YARIMAN BAKURA YA FASA KWAI YACE :~ Buhari Ne Ya Nemi A soke zaben Zamfara
Ku Tura A Social Media

* Na gaya wa Abdul’aziz Yari ya ki saurare na.

* Zan tsaya takarar Shugaban Kasa saboda wani Farin Balarabe ya tabbatar da zan ci zabe.

Bayan kamewa na tsawon lokaci, Sanata Ahmad Sani, Yariman Bakura, Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ya fasa kwai a kan dambarwar siyasar da ta share gami da jefa dukkan masu rike da madafun iko a Jihar Zamfara a kwandon tarihi ta hanyar bayyana sirrin da ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari bayan dawowarsa daga tafiya inda Shugaba Buhari ya gaya masa cewa bai aminta da abinda Gwamnan Jiharsa ya yi ba, kuma hakan ba zata sabu ba wai bindiga a ruwa.

Jin wannan maganar ke da wuya sai Sanatan ya garzaya gidan Gwamna Abdul’aziz Yari (a lokacin)na Abuja inda ya nemi ya tsegunta masa, amma ya hana shi ma ya yi magana ta hanyar neman ya janye hannunsa a cikin lamarin.

Sanata Ahmad Sani ya bayyana hakan ne a cikin wata zantawa da ya yi da majiyarmu har ma ya kara da cewa bayan kusan watanni biyu zuwa uku da Shugaba Muhammadu Buhari ya zo Jihar ta Zamfara ya maimaita wannan matsayar tasa a lokacin da yake ganawa da Sarakunan Jihar da wadansu jiga-jigan Jihar a asirce, wanda shi Yariman na Bakura na daga cikinsu. To amma kuma a lokacin bindin rakumi ya riga ya yi nisa da kasa.

Kin daga hannun ’yan takara da Buhari ya yi inji Yariman Bakura shi ne ya dada tabbatar da cewa akwai lauje cikin nadi dangane da takaddamar dake afkuwa.

Sanata Ahmad Sani ya  ce batawar da ya yi Tsohon Mataimakinsa Kuma Tsohon Gwamna Mamuda da kuma rashin son batawa da Gwamna mai ci(a lokacin) ne ya sa ya zura ido har sitiyarin motar siyasar ya tsunke ta kuma saki hanya ta fada daji inda ta yi kuli-kulin Kubura da kowa da kowa a jam’iyyar ta APC.

Wani batu kuma mai jan hankali da hirar ta tabo shi ne batun tsayawar Yariman Bakura takarar Shugabancin Kasa nan gaba inda ya ce wani Farin Balarabe da ya yi kama da rauhani ne ya gaya wa dan ajinsu a Makarantar Sakandare a yayin da ya je umra Makka shi da matarsa da diyarsa.

Daga nan sai Sanata Ahmad Sani ya cigaba da cewa “Batun takara a Jiha na gama insha-Allahu, amma sai ta Shugaban kasa idan Allah ya raya mu, domin na ga manya-manyan mutane da malumma sun soma jawo maganar cewa to ranka ya dade ka sani fa muna nan mun soma shirye-shirye...

A satin da ya wuce wani abokina da muka yi makarantar sakandare school da shi ... ya bugo min waya ya sheda mani cewa wani abin al’ajabi ya same shi, ya je Makka Umra, an gama Sallah yana fitowa a cikin harabar harami shi da matarsa da diyarsa sai ya ga wani Balarabe Fari tas...sai ya yi masu sallama da suka amsa sai ya ce ku ‘yan Zamfara ne ko...sai ya ce ina Sanata Ahmad Sani ya ce yana nan sai ya ce idan kun je ku fada masa cewa insha Allah zai yi mulkin Nijeriya...suna juyawa domin su tambaye shi sunansa sai ko kasa ko sama ya bace.” - Inji Sanata Bakura.

Har ila yau, Sanatan ya kuma ce da ya gaya wa wani wannan labarin shi ma ya ce ya yi mafarki inda ya ce ya gan shi ya zama Shugaban Kasa kuma an dauko shi a cikin wata bakar mota da tuta.

Ma’abota biybiyar wannan shafi na jaridar Dimokuradiyya mi zaku ce  a kan wannan bushara?

Shin Yariman Bakura zai zama Yariman dukkan Nijeriya?

In ya zama mi kuke so ya yi maku?

Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: