Friday, 1 November 2019
Tsohuwar Jaruma Hafsat Shehu Matar Marigayi Ahmed s Nuhu Tayi Aure

Home Tsohuwar Jaruma Hafsat Shehu Matar Marigayi Ahmed s Nuhu Tayi Aure
Ku Tura A Social Media

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Da yammacin wannan rana ta juma'a 1 ga watan Nuwamba ne aka daura auren tsohuwar jaruma kuma matar marigayi Ahmad S, Nuhu wato Hafsat Shehu a gidan su da ke unguwa uku a cikin garin Kano.

Duk da yake ba ta bayyana labarin auren nata Ba amma dai a lokacin daurin auren an ga fuskokin wasu daga cikin abokan sana'ar ta 'yan fim da suka hadu a gidan su amaryar inda ta shirya wani kwarya -kwaryan biki, don murnar auren nata.

Bayan rasuwar Ahmad S, Nuhu dai Hafsat Shehu ta yi aure inda ta auri wani mazaunin Abuja, koda yake auren bai je ko'ina ba suka rabu cikin rigima , kuma tun daga wancan lokacin dai bata yi wani Auren ba, duk da cewar Bata dawo harkar fim ba amma dai ba ta kara yin wani auren ba Sai yanzu.

Da fatan Allah ya ba su zaman lafiya da angon nata ya sa gidan zaman ta ne.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: