Friday, 22 November 2019
Sabuwar Soyayya Tsakanin Maishadda Da Jaruma Hassana Muhammad

Home Sabuwar Soyayya Tsakanin Maishadda Da Jaruma Hassana Muhammad
Ku Tura A Social Media
Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano Wata soyayya mai ban mamaki da aka dade ana yin ta tsakanin babban furodusa da ya fi kowa tashe a yanzu cikin masana'antar finafinai ta kannywood tare da sabuwar jaruma Hassana Muhammad a yanzu za a iya cewa ta fara bayyana, musamman ma dai idan aka yi duba da yadda alakar Maishadda da kuma jaruma Hassana Muhammad kullum ta ke daukar sabon salo.

 A baya dai ana daukar abin kamar da wasa, kasancewar furodusa Maishadda ba a san shi Da yin soyayya da matan da su ke cikin harkar fim ba, to Amma dai a wannan lokacin za a iya cewa Hassana ta kama shi a wuya domin kuwa wani daga cikin makusantan sa ya shaida mana cewar Akwai kyakyawar alaka tsakanin su, kuma har soyayyar ma dai akwai ta, sai dai ba su cika son a gane hakan ba. Amma daga yadda jarumar ta ke dora hoton sa da yadda shi ma ya ke dora hoton ta a shafin Dandalin sada zumunta ya kara tabbatar wa da muta ne cewa alakar soyayya mai karfi ta ginu a zukatan su. Ba wani Abu ne sabo ba soyayya tsakanin jaruma da wani babban jarumi ko furodusa ko Darakta, amma dai ma fi yawan soyayyar ta kan kare ne kamar a Teburin mai shayi, domin kuwa mafi yawan soyayyar 'yan fim ba ta kai su ga yin aure, sai an ci sa' a ma a ke rabuwa Lafiya amma da dama ana rabuwa ne cikin tashin hankali da tona wa juna asiri.

 Da fatan dai wannan soyayyar ta Maishadda da Hassana Muhammad zata haifar da da mai ido, Domin jin hakikanin maganar soyayyar da ke tsakanin Maishadda da Hassana Muhammad, mun yi ta kokarin jin ta bakin Abubakar Maishadda, amma tsawon wuni guda ba mu same shi ba. Mun aike Mishi Sakon Karta Kwana amma dai Shiru, Ita kan ta Hassana Muhammad din mun yi ta kiran wayar ta ba ta shiga ba. Amma dai mu na nan mu na ci gaba da bi biya, duk lokacin da mu ka ji daga gare su, za mu Sake kawo muku. Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya


Share this


Author: verified_user

0 Comments: