Friday, 29 November 2019
Madallah: Sheikh Minista Pantami ya hana shugaba Buhari gaisawa da mata (Kalli Bidiyo)

Home Madallah: Sheikh Minista Pantami ya hana shugaba Buhari gaisawa da mata (Kalli Bidiyo)
Ku Tura A Social Media
A wani sabon salon a hani mummunan aiki, tare da umarni da kyawawan ayyuka, babban malamin addinin musulunci kuma minista a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sheikh Isah Ali Pantami ya yi gwaninta.

Shehin malamin, wanda shi ne ministan sadarwa da tattalin arzikin kimiyyar zamani, ya hana shugaban kasa Muhammadu Buhari gaisawa da wata mata ne yayin wata ziyara da shugaban ya kai wani wurin taro.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari zai shilla kasar Equatorial Guinea daga nan zai wuce Daura

Cikin wani bidiyo da a yanzu ya karade shafukan yanar gizo an hangi shugaba Buhari ya fito daga cikin motarsa, yayin da manyan jami’an gwamnati suka yi layi ta hannun damansa suna jiran isowarsa domin su tarbeshi.

Isowar shugaban kasa keda wuya, sai Malam Pantami ya tare shi, inda ya bashi hannu suka yi musabaha, yayin da sauran jami’an ke tsaye a kan layi, inda bayan Buhari ya baiwa jami’in farko dake kan layin hannu, sai Pantami ya shiga gabansa yak are matar dake ta biyu a layin, sa’annan ya nuna ma Buhari hannu ya yi gaba.
Don haka babu yadda shugaba Buhari ya iya, sai dai ya yi gaba, inda ya waiwayo ya gaisa da matar da fatar baki, yayin da matar ta rusuna kadan, daga nan Buharin ya cigaba da gaisawa da sauran jami’an dake kan layi.

Idan za’a tuna, a kwanakin baya ne babban malamin ya kirkiro wani sabon salon sigar gaisawa da mata ba tare da an hada hannu ba wacce yayi wa lakabi da “wireless greetings”.

A cewar malamin hakan sabuwar fasaha ce wacce ke ba mutum damar gaisawa ba tare da cudanya ba sannan kuma an kiyaye dokokin Allah a ciki.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: