Uncategorized

Ma’aurata : Sunnoni 20 Na Soyayyar Aure

Na daya (1) Yin  murmushi idan ka  kalli fuskar matarka.
Manzon Allah (saw) yace murmushinka a fuskar Dan uwanka sadaka ne. Tirmiziy

Na biyu (2) Sunbatar mace idan zaka fita (kiss). Nana Aisha tace MANZON ALLAH (saw) yana sunbatar matarsa idan zai fita. Abu Dawud

Na uku (3) Amincewa da ita da rashin tuhumar ta. Manzon Allah (saw) ya hana mutum ya dinka fadowa matansa da daddare, kada  ya dinka bin diddiginsu da zargi. Muslim ne ya Ruwaito

Na hudu (4) Yin sallar dare tare da iyali.
MANZON Allah (saw) yace: Allah yaji kan mutumin da ya tashi da daddare yana sallah, kuma ya tashi matarsa, idan taki ya yayyafa ruwa a fuskarta – Abu Dawud

Na biyar (5). Nuna damuwa da halin da matar mutum take ciki, na rashin lafiya da bata kulawa a Wannan lokacin, kamar yadda Annabi (saw) yake nunawa iyalinsa.

Na shida (6), Ka fada mata kana kaunar ta domin taji dadi, kamar yadda aka tambayi Annabi (saw), wa yafi so? Sai yace Aisha.

Na bakwai (7) Girmama iyayenta da danginta da kawayenta, kamar yadda Annabi (saw) yake yiwa kawayen Nana Khadijah bayan rasuwarta.

Na takwas (8),  Yi mata godiya da yabawa akan girki da kwalliya, domin taji dadi.

Na tara (9), kada ta kawo abinci ko abin sha ya kushe, kamar yadda Annabi (saw), baya kushe abinci, idan yayi masa yaci, idan baiyi masa ba ya barshi.

Na goma (10). Ya dinka yin hira da tattaunawa da iyalinsa, da kuma bata damar fadar raayinta. Kamar yadda Annabi (saw) yake bawa matansa.

Na sha daya (11),  Lallashin mace idan ta shiga damuwa, da kwantar mata da hankali idan ta shiga halin tsoro da firgici. Kamar yadda Annabi (saw) yake yiwa iyalansa.

Na sha biyu (12), Kauda kai daga kura-kurai da tuno alkhairinta a lokacin da aka sami matsala. Kamar yadda Annabi (saw) ya koyar kuma ya nuna a  aikace, yace:  kada mumini yaki mumina saboda wani halinta da baya so. Domin idan yaki wani halin nata, to tabbas zafi so wani halin da take dashi. Muslim ya ruwaito

Na sha uku (13), ya dinka kiranta da suna mai dadi kamar yadda Annabi saw, yake kiran Aisha da Humaira ko kuma Aish ko Ayish.

Na sha hudu(14),  ya dinka yi mata tsafta da  kwalliya kamar  yadda shima yake so ya ganta.

Na sha biyar (15), ya dinka taimaka mata aikin gida, kamar yadda Annabi saw yake taimaka iyalansa.

Na sha shida (16), yin wasa da iyali,  kamar yadda Annabi yake yi kuma ya koyawa Jabir cewa idan ya auri budurwa zaiyi mata wasa itama tayi masa,  yayi mata dariya ita ma tayi masa. Bukhari da Muslim suka ruwaito .

Na sha bakwai (17),  yin wanka tareda Iyali  kamar yadda Annabi (saw) yake yi.

Na sha takwas (18),  ya dinka kwanciya yana tada kai da cinyar matar sa, kamar yadda Manzon Allah (saw) yake yi, tare da Aisha ko tana cikin jinin al’ada.

Na sha Tara (19),  YA rika bata abinci a bakinta da cokali ko da hannu,  kamar yadda aka fahinmta daga hadisin Bukhari da Muslim,  cewa , Allah zai baka lada, har lomar da kake sanyawa a bakin matarka, wasu malamai sun fassara cewa, ka ciyar da ita kuma ka bata a baki da hannunka, 

Na ashirin (20), Idan matar ka taci abinci ta rage,  ka dauka kaci ragowar, zataji dadi. Kamar yadda Nana Aisha tace idan naci abinci, Manzon Allah saw yana ci, a inda na saka bakina, haka idan na sha abin sha,  yakan sha ta inda na sha. Muslim ya Ruwaito.

Sheik Daurawa.

Allah ya bamu ikon kamantawa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button