Friday, 29 November 2019
Kyawawan Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa Da Suka Yi Auren soshiyal midiya sun Bayyana Labarin soyayyar su Mai Ban mamaki

Home Kyawawan Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa Da Suka Yi Auren soshiyal midiya sun Bayyana Labarin soyayyar su Mai Ban mamaki
Ku Tura A Social Media
Komai da zaka gani ya faru, akwai tushenshi ko mafarin shi, ballantana aure ko soyayya Legit ta ruwaito.

- Wasu masoyan kan hadu a makaranta, titi, biki, asibiti ko kuma dai a kasuwa

- Ga wasu masoyan da suka ci ribar soyayya ta hanyar aure, sun bada bayanin yadda suka hadu da juna

Bahaushe dai na cewa soyayya gamon jini. Ba a haduwa da saurayi yau a aureshi gobe. Ko kuma zamu iya cewa, kowanne masoya da ka gani, toh tabbas akwai wani labari mai dadi ko akasin hakan da ya zamo tushen soyayyar tasu.

Wasu tarin ma’aurata sun bayyana yadda suka hadu da juna a kafafen sada zumuntar zamani tare da labarin soyayyarsu.


Wata mai suna Ummieta Rabiu, ta yi bayanin yadda suka hadu da nata mijin kuma rabin rayuwarta. Ta hadu dashi ne a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita. Tana da shekaru 17 inda yake da 23. Sun yi soyayyar shekaru bakwai inda daga baya suka angwance. A halin yanzu dai shekarunsu hudu da aure cikin zaman lafiya da kaunar juna.


“Mun hadu ne a tuwita, ina da shekaru 17 shi kuma yana da 24. Mun yi soyayyar shekaru 7 inda daga baya muka yi aure. A halin yanzu muna da shekaru 4 da aure.” In ji Ummeeta.


Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya
Ita kuwa Khadija ta ce: “Mun hadu a tuwita a shekaru 8 da suka gabata. Ina da shekaru 20. Mun yi shekaru hudu da aure, amma babu abinda zan ce sai godiya ga Allah domin kuwa ya albarkace mu da ‘ya mace.”Malam Anas kuwa yayi bayanin cewa, ya hadu da matarshi uwar ‘ya’yan shi biyu a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook ne. Tana da shekaru 21 inda shi yake da 25. Sun yi aure a 2012. A halin yanzu shekarunsu bakwai da aure. Allah ya albarkacesu da ‘ya’ya biyu.
Wata kuwa mai suna Cicaeda kamar yadda ya nuna a shafinta na tuwita, ta ce “Mun hadu dashi ne tun muna makarantar sakandire. Ina da shekaru 13 inda yake da 16. Shekaru 16 kenan da suka gabata. Mun yi aure tun shekaru 7 da suka gabata. Hukunci mafi muhimmanci da muka yanke.”


Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: