Wednesday, 27 November 2019
KO 'YAR GWAL SAI HAKA: Wa Zai Biya Naira Dubu Goma Domin Jin Tarihin Zahra Buhari?

Home KO 'YAR GWAL SAI HAKA: Wa Zai Biya Naira Dubu Goma Domin Jin Tarihin Zahra Buhari?
Ku Tura A Social Media

Daga Datty Assalafiy

Wai Zahra Buhari za ta shirya wani taro a Abuja na wayar da kai da fadin tarihin rayuwarta,  kudin shiga dakin taron naira dubu goma (10,000), taron zai gudana ranar Asabar mai zuwa

Na ga ana cecekuce ana kokarin alakanta abin da shugaba Buhari, ita kuma ana zaginta wai Barauniya, babu ruwan shugaba Buhari da wannan taron, haka ne ko ni a gurina kudin ya yi yawa tunda ba lada za a samu da ganin 'yar gidan shugaban kasa ba.

Wannan abu ne mai sauki, ganin damar mutum ne ya ganta, amma maimakon mutum ya kashe naira dubu goma saboda ganin 'yar shugaban kasa ya fi dacewa ya dauki kudin ya kai gidan marayu, idan ba haka ba wannan zai iya zama almubazzaranci.

Sannan Zahra yanzu ba'a karkashin ikon mahaifinta take ba, tana karkashin ikon mijinta ne Ahmed 'dan gidan attajiri Indimi, idan laifi za'a gani sai dai a ga laifin mijinta amma ba shugaba Buhari ba.

Ba Zahra ba wallahi ko shugaba Buhari ne da nake tunanin zan iya sadaukar da rayuwata a kansa zai shirya taro indai sai na biyu dubu goma na ganshi na hakura da ganin nasa a duniya, ma hadu a Aljanna.

Allah Ya shirya.

Wannan labari ba ƙanzon kure ge bane sahihin labari ne wanda a shafinta na Instagram ta fitar da wannan labari.

View this post on Instagram

There is always a journey before the journey. An extending grace of choice before acceptance and approval. However, there will always be a story of success and accomplishments despite challenges and odds. I have my story to tell. I believe you do too. I want to tell my story of confidence and success despite the harsh reality of cyber bullying. I have always been passionate about sharing personal experiences and I believe that we cannot get to a space of connection with others until we share who we are. My story of confidence and success will be shared with you for your inspiration and influence. Come have an amazing time with me as you hear authentic story of self development that will feed your passion, clarity and allow you make choices for your growth. The first 15 people to register and pay will get a seat for just 6k ! Make sure you send that email now! I can’t wait to meet you all ❤❤ #inconversationwithzahra #zahrabuhari
A post shared by 𝐙𝐚𝐡𝐫𝐚 𝐌 𝐁𝐮𝐡𝐚𝐫𝐢-𝐈𝐧𝐝𝐢𝐦𝐢 (@mrs_zmbi) on

Share this


Author: verified_user

0 Comments: