Tuesday, 19 November 2019
Ina son Na Yi suna Na Zama kamar Ali Nuhu da Saif Alee khan - Shamsu Dan Iya

Home Ina son Na Yi suna Na Zama kamar Ali Nuhu da Saif Alee khan - Shamsu Dan Iya
Ku Tura A Social Media
Burina na zama kamar Ali Nuhu ko Saif Alee khan” Inji Matashin jarumin da ake yayi kuma yake tashe a duniyar fina-finan hausa Shamsu Dan Iya.Northflix ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a wata zantawar da suka yi da wakilin mu ranar Juma'a 15th November 2019. Ida jarumin ya amsa tambayoyi cikin raha da nishadi.

Ya fara da cewa shi dan garin kaduna ne kuma a can aka haife shi, Kano kuma da yake zaune yanzu sana’a ce ta kai shi kuma Alhamdulillah ya fara samun abinda ya ke so dai dai gwargwado.

Jarumin ya yi fina-finai sun Kai guda bakwai wayan da suka yi fice kamar su Kanina, Sareena, Kar Ki Manta Da Ni  da sauransu.

Wakilin mu ya tambaye shi ko menene babban burin sa a  wannan harka day a shiga? Ya amsa da cewa

“Gaskiya babban buri na shi ne ace yau naga na zama daya daga cikin manyan jaruman da duniya ta ke kallon su kuma ta ke jinsu, shi ne ya sa na ke koyi da manyan gwanayen jarumai na duniya Ali Nuhu da Saif Alee khan jarumin fina-finan Indiya.

Kuma ina so na zama daya daga cikin jaruman dake fadakarwa tare da nishadantarwa don shi ne ma abinda ya ba ni sha'awa na shiga harkar fim. Tabbas ina jin dadin abinda na ke yi tunda sana’a ce kuma ina yiwa Allah godiya da irin ni'imar da ya yi min. Ina da sana’a wacce ta ke taimako na kuma na ke samun abubuwan more rayuwa dai dai gwargwado Allah ya wadata ni dasu.” Inji Jarumin

Ko wanne kalubale ka ke fuskan ta a masana’antar ta kannywood?

Ya kammala da cewa; “Na samu  kalubale ko kuma ince Ina kan samu  tun da zaka ga ciki da wajen Kannywood kana burge mutane wasu kuma baka burge su dama haka duniya ta ke baki daya.  Amma ina yiwa mutune albishir da cewa ana nan ana gyare gyaren abubuwan da za su sauya masana’antar kannywood ta kai wani babban mataki a duniya, kuma inaso masoyan kallon Fina-finan Hausa da su rika bada gudunmawa wajen karbar duk wasu chanje chanjen da ake samu na kai fina-finai sinima da kuma daura su a yanar gizo ta hanyar da za a Kalli fim cikin sauki a duk inda mutun yake, kamar su Northflix da sauransu.” A cewar Dan iya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: