Monday, 25 November 2019
Fati Nijar Ta Samu Mukamin Gimbiyar Mawakan Turai

Home Fati Nijar Ta Samu Mukamin Gimbiyar Mawakan Turai
Ku Tura A Social Media


Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

A kowanne lokaci dai tauraruwar fasihiyar mawakiya Fati Nijar sai kara dagawa ta ke yi, a fagen waka. Domin kuwa a baya ana yi mata kallon makawiyar Afirka, amma dai a yanzu likkafar ta ta kara ci gaba zuwa kasashen Turai, in da aka nada ta a matsayin Gimbiyar mawakan Kasar Turai,.

A satin da ya gabata ne Fati Nijar ta amsa gayyatar da sarkin Hausawan kasar Turai Mai Martaba Alhaji Dakta Surajo Jankado Labbo ya yi mata zuwa birnin Paris na Kasar Faransa in da su ke gudanar da bikin al'adun Hausawa mazauna Turai, a duk shekara.

Taron dai yana samun halartar dukkanin Hausawa na kasashen Turai in da su ke haduwa domin gudanar da bikin al'adun Hausawa, domin tuna al'adun su na gida.

A wannan shekarar dai Fati Nijar ta samu halartar bikin, da aka gudanar a jiya asabar, kuma a wani bangare na bikin ne aka nada Fati Nijar din a matsayin Gimbiyar Mawakan Kasar Turai, in da aka saka Mata wata alkyabba ta alfarma, domin karrama ta.

An dai yi bikin an gama lafiya, kuma a lokacin da su ke magana da wakilin mu Mukhtar Yakubu ta waya, Ta bayyana godiyar ta ga Allah bisa wannan matsayi da ta samu, sannan ta yi godiya ga Hausawa mazauna kasar Turai, musamman ma Sarkin su, Alhaji Dakta Surajo Jankado Labbo.

Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: