Sunday, 24 November 2019
Dalilin Da Yasa Nayi Hijira Daga Kano zuwa Kaduna ~ Adam A zango

Home Dalilin Da Yasa Nayi Hijira Daga Kano zuwa Kaduna ~ Adam A zango
Ku Tura A Social Media


Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Adamu Abdullahi wanda aka fi sani da Adamu Zango ya bayyana cewa ya kauracewa jihar Kano da zama zuwa jihar Kaduna, har sai zuwa nan gaba.
Jarumin ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da yayi da tashar Radio France International (RFI), inda yayi karin haske kan matakin da ya dauka na ficewa daga masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood.

Adamu Zango ya bayyana cewa sakamakon rashin adalci da yake samu da sauran ‘yan uwansa masu fina-finai a Kano ya sanya shi yanke wannan hukunci, kuma a yanzu haka yana cigaba da yin fina-finan sa, sannan ya baiwa hukumomin tace fina-finai na kasa don su duba masa.
Sai dai jarumin ya ce hakan bai shafi masoyansa na jihar Kano ba.
Ku Dannan kan wannan hoto domin saurarin muryasa.
Mun samu wannan murya maganarsa daga jaridar Dala fm kano


Share this


Author: verified_user

0 Comments: