Thursday, 28 November 2019
Buhari Ya Bukaci Majalisa Ta Bashi Damar Karbo Bashi

Home Buhari Ya Bukaci Majalisa Ta Bashi Damar Karbo Bashi
Ku Tura A Social Media
Shugaba Muhammadu Biuhari ya nemi Majalisar Tarayya ta sake dubawa tare da sahhale kudirin neman bashin da ya aika wa majalisa ta takwas mai suna 2016-2018 External Borrowing Plan,bbchausa na ruwaito.

Shugaban ya gabatar da bukatar ne a wata wasika da ya aike wa 'yan majalisar kuma aka karanta ta a yau Alhamis a zauren majalisar.
Buhari ya bayyana a cikin wasikar cewa za a karbo bashin ne saboada kammala wasu ayyuyka da aka zayyana a cikin kudirin neman bashin na shekarar 2016-2018.

Ya kuma yi bayanin cewa majalisa ta takwas, karkashin jagorancin Abubakar Bukola Saraki, wani bangare kawai na dokar ta amince da shi, "abin da ya kawo tsaiko ga wasu daga cikin ayyukan raya kasar da gwamnatinsa ke yi," in ji Buhari.

Shugaban ya ce ayyukan da rashin amincewa da kudirin ya shafa sun hada da hakar ma'adanai da wutar lantarki da lafiya da noma da ruwan sha da kuma ilimi.

"Saboda haka na hado maku da kwafin bayanai daga Ministar Kudi da Tsare-Tsare game da ayyukan da muke bukatar gudanarwa idan kuka amince da kudirin 2016 – 2018 External Borrowing."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: