Labarai

Babban Burina Na Inganta walwalar Duk Wani Dan Najeriya – Inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya himmatu matuka wajen habbaka walwalar yan Najeriya tare da inganta rayuwarsu, kamar yadda ya bayyana ma taron gwamnonin jam’iyyar APC a garin Jos na jahar Filato Legit na ruwaito.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaban kasa ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin taron tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC inda aka tattauna a kan tsare tsaren gwamnati.

Buhari, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana cewa gwamnatinsa na alfahari da nasarorin da ta samu na tayar da komadar tattalin arzikin kasa bayan shiga halin tabarbarewa a baya.

Shugaban kasa yace a yanzu haka Najeriya ta hau hanyar samun cigaba mai daurewa tun shekaru hudu da suka gabata, musamman ta bangaren cigaban al’umma, samar da manyan ayyuka da kuma alkhairai daban daban.

Sakamakon fahimtar muhimmancin mawuyacin hali da jama’a ke shiga, musamman wadanda ibtila’I ko rikici ya rutsa dasu, na samar da sabuwar ma’aikata wanda na mika ma jami’in gwamnati mai mukamin minista domin ya jagoranta.

Wannan ya nuna manufar gwamnatina na rage radadin matsalolin da yan Najeriya suke fuskanta, musamman marasa karfi. Alkalumma sun tabbatar da tun daga shekarar 2015, gwamnatinmu ta samu cigaba a fannoni daban daban, kuma a shirye muke mu ninka kokarinmu.” Inji shi.

Shugaban kasa ya jaddada ma gwamnonin APC manufarsa na kawo karshen matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar nan. Sa’annan ya danganta dukkanin nasarorin daya samu ga goyon bayan da gwamnoni suke ba shi.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar gwamnonin APC, Atiku Bagudu ya bayyana cewa suna hada kai da gwamnatin tarayya ne domin su inganta rayuwar dan Najeriya. Taron ya samu halartar gwamnonin APC 8 da mataimakan gwamnoi guda 3, sai kuma ministoci 2, da shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?