Sports

Ashe Malam Ya Iya kwallo – Ministan sadarwa, Sheik Pantami, Ya taka leda (Bidiyo)

A yau ne ministan sadarwa da tattalin arzikin ilmin zamani, Dakta Isa Ali Pantami, ya taka leda a taron gwajin fasahar 5G da kamfanin sadarwan MTN tayi a ofishinta dake Abuja.

Shehin Malamin kuma hazikin masanin ilimin kwamfutan ya halarci taron tare da shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar Danbatta, da wasu masu ruwa da tsaki a bangaren sadarwa.

TechEconomy.ng ta bada rahoto a watan Agustan 2019 cewa hukumar NCC ta ce za’a gwada fasahar 5G a Najeriya.

Kalli bidiyon:

— Fed Ministry of Communications & Digital Economy (@FMoCDENigeria) November 25, 2019

A bangare guda, Ministan sadarwa, Sheikh Dakta Isa Ali Pantami, ya yi gargadi ga wasu marasa kishin kasa dake kokarin yiwa ma’aikatarsa zagon kasa kan ayyukan walwalan jama’an da suke yiwa yan Najeriya.

Malam Pantami, ya yi wannan gargadi ne ta bakin mai magana da yawunsa, Uwa Suleiman, a jawabin da ta saki ranar Litinin a Abuja.

A jawabin yace binciken da aka kaddamar kan wasu masu almundahana ya sa suna kokarin yada labaran karya kan ma’aikatar.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button