Uncategorized

Yadda Iyaye Ke Haddasa Mutuwar Auren ‘Ya’yansu Da Kansu

Leadership hausa

kowace uwa ta gari shi ne, ta ga cewa ta aurar da diyarta, sannan ta samu zaman aure na jin dadi da kuma kwanciyar hankali, don haka ne ma iyaye suke maida hankali wajen ganin sun aurar wa ‘ya’yansu mazaje na gari.

 Iyaye mata su ne wadanda suka fi kusanta da ‘ya’yansu musamman ‘ya’ya mata, don haka ne yawancin iyaye suke da burin ganin cewa sun yi wa ‘ya’yansu tarbiya ta gari kafin su aurar da su.

 Iyaye mata masu cusa wa ‘ya’yansu tarbiya ta gari ba su fitowa da wani rashin kyautawa a fili da zai nuna wa ‘ya’yansu musamman mata.

 Ba sa nuna wa a zahiri idan suna da matsala da mahaifinsu, ko kuma yin wata kalma ko dabi’a a gaban ‘ya’yansu na yadda za su tozarta mazansu a gaban ‘ya’yansu mata.

A yayin da irin wadannan iyayen na gari suke kokarin cusa wa ‘ya’yan mata dabi’a ta gari, wasu iyayen kuma kokarinsu shi ne, su yi wa ‘ya’yansu mata hudubar shaidan kamin lokacin aurensu da kuma bayan auren nasu.

Wadannan iyayen suna iya koya wa ‘ya’yansu dabi’u na banza ne ko dai ta hanyar mu’amularsu da mazajensu wato iyayen ‘ya’yan nasu, ko kuma ta zaunar da ‘ya’yansu domin yi musu darasin da koyarwar shaidan.

 Akasarin matan da suka rabu da mazajensu a wannan halin da muke ciki sun tabbatar da cewa, babu abin da ya kashe masu aure sai irin huduba mara amfani da iyayensu ko masu rike da su suka yi masu kamin aurensu.

Wanda hakan ya jefa su cikin dana sani kuma suke zargin iyayen nasu da yi masu hudubar banza. Ba wata sabuwar kalma bace a wajen iyaye mata su ce wa ‘ya’yansu mata, “namiji ba dan goyo ba ne.

 Duk wanda ya rike namiji uba zai mutu maraya” wadannan kalmomin da irerensu sun yi matukar tasiri a zukatan ‘ya’ya mata tun suna ‘yan mata har lokacin aurensu kai har kuma lokacin da suma za su aurar da ‘ya’yan mata wadannan kalmomin yana ransu kuma a kullum shi suke yi wa ‘ya’yansu mata huduba da shi.

Bari mu dauki kalmar da kowa ya san mata suke amfani da ita na cewa namiji ba dan goyo ba ne. Wannan kalmar ta yi wa ‘ya’ya mata illar da ya jefa su cikin rashin samun zaman jin dadin aure.

 Haka kuma wannan kalmar ta ingiza keyar matan aure da dama zuwa gidajensu bayan aurensu ya mace.

 Illar da wannan kalmar ke yi wa ‘ya’ya mata shi ne, dauka suke kuma babu wani gwaninta da mace a rayuwarta za ta iya yi wa mijinta harma ya yaba mata ko ya ganta da mutunci.

 Ba kuma komai ya sa shaidan ya cusa wa mata wannan muguwar kalmar ba, sai saboda tsabar son rai irin na mata a lokacin da suka ga cewa namiji zai yi musu kishiya.

 Yana da kyau ‘yan’uwa mata su fahimci cewa yi wa namiji biyayya ko ladabi a matsayinki na matarsa, abu ne da ya wajaba a gare ki, bawai saboda kina yin masa ba ne domin kada ya karo miki kishiya ko kuma domin ki samu damar mallakarsa.

Idan mata suka kudiri wannan a ransu suka fahimci cewa yi wa miji ladabi da biyayya abu ne da ya wajaba ba wai suna yi ba ne domin neman wata alfarma ba, kamar yadda dan’adam yake bautawa Ubangijinsa, saboda bautar zai kara wa Ubangijin komai ba daga gare shi babu wani sauran takaici a wajen ‘ya mace.

Haka kuma iyaye mata suke nuna wa ‘ya’yansu cewa, kada su nuna wa mazansu soyayya, domin a tasu hudubar, idan mace na nuna wa namiji so yana iya wulakantata, amma idan tana shareshi tana nuna wa tamkar ba ta son sa zai fi samun zaman lafiya.

Wannan hudubar tasu ta yi kama da tunanin wasu mazan da suke cewa ba a sakar wa mace fuska.

Wannan hudubar tana taimakawa wajen kawo rashin jituwa a gidajen mata da dama wadanda suka dauki wannan nasihar ta iyayensu mata a matsayin wata shawara ce ta gari, wanda daga bisani ta kai su ta baro bayan da aka sako su daga gidajen aurensu, suka dawo gaban iyayen.

Irin wannan hudubar da ake yi wa mata kamin su shiga gidan miji na kada su sake su nuna wa mazajensu soyayya a fili, yana jefa matan cikin wani hali.

Masu irin wannan matsalar ta hudubar iyaye mara kan gado, ba sa iya zaman aure domin iyayen sun bata rayuwarsu na aure. Iyaye mata su ji tsoran Allah, su daina mai da ‘ya’yansu zawara tun Yanzu.

Share this:

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button