Tuesday, 8 October 2019
VIdeo : GIDAN BADAMASI (Episode One) Latest Hausa Series

Home VIdeo : GIDAN BADAMASI (Episode One) Latest Hausa Series
Ku Tura A Social Media#GidanBadamasi sabon fim din wasan barkwanci ne da ake dauki-ba-dadi a tsakanin wasu irin 'ya'ya masu kunnen kashi da mahaifinsu Alhaji Badamasi. Badamasi dattijon attajiri Dan kimanin shekaru saba'in yayi aure da dama a rayuwarsa, inda ya haifi 'ya'ya masu yawan gaske, wasu ma bai San Ina suke ba a halin yanzu. A wannan wasan kwaikwayo an fara Kai ruwa rana ne daga lokacin da Alhaji Badamasi ya kasa cika alkawarin kudin da ya yiwa 'ya'yansa. Yaki ya barke tsakanin marowacin uba da handamammun 'ya'ya
#GidanBadamasi.

 Fim ne na barkwanci mai dauke da nishadantarwa da ilmantarwa ta hanyar amfani da gwanayen 'yan wasan barkwanci ta yadda mutum zai yi ta zura idanu yana jiran ganin abin da zai faru a nan gaba. \
#GidanBadamasi. Sabon shirin zai fara zuwa a makon farko na watan Octoba.
A tashar arewa24channel
Ga bidiyon nan domin ku kalla daga channel din Falalau Dorayi.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: