Wednesday, 9 October 2019
Najeriya za ta kaddamar da kimiyyar sadarwa mai karfin 5G - Dr. Pantami

Home Najeriya za ta kaddamar da kimiyyar sadarwa mai karfin 5G - Dr. Pantami
Ku Tura A Social Media


Ministan sadarwa a Najeriya, Dr. Isa Ali Pantami, ya bayyana cewar; Najeriya ta fara gwaje-gwaje a matakin farko don kawo kimiyyar sadarwa mai karfin 5G a Najeriya.

Ministan, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron muhawarar "GITEX Showdown Debate": mai taken 'Are we at risk of the next cyber-pearl-harbor?’, wanda ya gudana a kasar hadaddiyar daular Larabawa (Dubai)

A cewar sa, an tsara kimiyyar sadarwar mai karfin 5G ne bisa jagorancin ma'aikatar sadarwar Najeriya tare da hukumar dake kula kamfanonin sadarwa na kasa (NCC) da kuma hadin guiwar wasu hukumomin tsaron Najeriya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: