Wednesday, 9 October 2019
Hotuna: Tsofaffin jaruman Kannywood mata guda 15 da suka dawo Harkar fim Bayan mutuwar Auren su

Home Hotuna: Tsofaffin jaruman Kannywood mata guda 15 da suka dawo Harkar fim Bayan mutuwar Auren su
Ku Tura A Social Media
Kamar yadda muka ruwaito muku a rahoton dawowar jaruma Farida Jalal harkar fim, cewa yanzu kamar yayi ne ake na dawowar tsofaffin matan da suka taka rawa a masana'antar Kannywood, hakan yasa muka bincika muka zakulo muku wasu daga cikin jaruman Kannywood mata da suka taka rawar gani a baya a masana'antar ta Kannywood kana kuma bayan mutuwar auren su suka dawo harkar.

Koda yake wasu bamu da tabbacin sun dawo fim din ka'in da na'in kasancewar bamu gansu cikin fim ba amma akan gansu jefi-jefi cikin 'yan fim din, amma kuma da yawan su sun tabbatar da dawowar su inda wasu suka bayyana da bakin su wasu kuma kawai sai ganin su aka cigaba da yi a cikin fim.


Ga dai jerin jaruman a kasa:


1. Hadiza Kabara


Hadiza kabara
2. Hafsat Shehu


Hafsat Shehu
3. Fati Muhammad


Fati Muhammad
4. Maijidda Abbas


Maijidda Abbas
5. Fati Baffa Fage


Fati Baffa Fage
6. Farida Jalal


Farida Jalal
7. Rukayya Dawaiya


Rukayya Dawayya
8. Saima Muhammad


Rukayya Dawaiya
9. Samira Ahmad


Samira Ahmad
10. Fauziyya Mai Kyau


Fauziyya Mai Kyau
11. Sadiya Gyale


Sadiya Gyale
12. Sadiya Kabala


Sadiya Kabala
13. Maryam Ab Yola


Maryam Ab Yola
14. Tumba Gwaska


Tumba Gwaska
15. Fati KK


Fati KK
Maryam Ab Yola, Sadiya Kabala da Tumba Gwaska ba za a kira su da tsofaffin jarumai ba kasancewar ba wacce ta shekara goma a masana'antar a cikin su sai dai sun shiga wannan lissafi ne saboda sun yi aure kuma sun fito sun cigaba da harkar.

Haka zalika ba wai ana nufin wadannan sune kawai jaruman Kannywood mata da su kai aure suka fito ba amma sune ake kyautata zaton sun dawo harkar fim, kuma ana ganin su ne a cikin dukkan sha'ani na 'yan fim.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: