Tuesday, 22 October 2019
Hafsat Idris Ta Zama Jakadiyar Kamfanin Delfin

Home Hafsat Idris Ta Zama Jakadiyar Kamfanin Delfin
Ku Tura A Social Media
Shafin Northflix ya wallafa.
A makon da ya gabata Jaruma Hafsat Idris ta samu jakadancin wani kamfanin kayan gyara jiki mai suna DELFIN, inda ta wallafa hoton ta dauke da Kayayyakin kamfanin a shafin ta na Instagram tana nuna farin cikinta da godiya ga Allah da kuma dun bin masoyan ta.

Baya ga haka Jarumar tana jakadanci da wasu kanfanunuwa kamar su Golden Penny masu yin Taliya, da kuma Dawa Vita, da sauransu.

Jarumar ta bayyana mana cewa ta fara samun irin wannan daukakar ne tun lokacin da aka fara haska fuskan ta a finafinai cikin shekaru uku da suka shude." Inji jarumar.

Ta kuma Kara da cewa tana mai godiya ga Allah da kuma Dukkanin daukacin Masoyanta akan irin gudumawar da su ke bata har ya kai ta ga irin wannan matsayin da take kai yanzu. Ta na mai ba masoyan ta hakuri akan rashin amsa sakonnin da suke turo mata akan  lokaci.

“kuyi hakuri ayyuka ne suka mun yawa”. Inji Hafsat Idris

Fim dina KAWAYE, ZAN RAYU DAKE, WAZEER suna nan tafe a kasuwa nan ba jimawa ba, masoya na suyi hakuri akan Shiru da suka jini kwana biyu, halin da ake ciki ayan zu ba kasuwa ne, ko anyi fim ba`a samun riba Sai faduwa amma ana kan gyararraki yanda komai zai daidai ta nan ba da dadewa ba cikin yardar Allah." Inji Jarumar.

Ta kamala da cewa “Inayi wa masoya kallon Finafinan Hausa albishir da Sabbabin fina finan da zan yi cikin shekarar nan da kuma shekarar da zamu shiga in Allah ya kaimu, Aciki akwai MATA DA MIJI da sauran su.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: