Monday, 14 October 2019
Hafsat Idris (Barauniya) Ta Lashe Kyautar Jarumar Kannywood

Home Hafsat Idris (Barauniya) Ta Lashe Kyautar Jarumar Kannywood
Ku Tura A Social Media


Fitacciyar ‘yar wasar Hausa Fim din nan wato Hafsat Idris wacce aka fi sani da Hafsat Barauniyya ta lashe kyautar Jarumar Kannywood wato Award ɗin ‘Best Kannywood Actress’ da kuma dayar kyautar da aka yiwa take da ‘Face of Kannywood’ a bikin gasar da City People Movie Awards na 2019 ke shiryawa a Legas.

Rahotanni da suka fito daga garin Legas din, ya nuna cewa; Jarumar ta fashe da kuka a yayin da take karbar kyautar daga hannun Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya daga jihar Kaduna, Kwamared Shehu Sani wanda ya mika mata a madadin wadanda suka shirya taron.Share this


Author: verified_user

0 Comments: