Wednesday, 2 October 2019
Dalilin Sanyawa Masana'antar Shirya Finia Finan Hausa suna "Kannywood" - Ali Nuhu

Home Dalilin Sanyawa Masana'antar Shirya Finia Finan Hausa suna "Kannywood" - Ali Nuhu
Ku Tura A Social Media
Akwai matukar wahala a rasa fina finan Hausa a gidan Malam Bahaushe, da ma wanda ba Bahaushe ba amma yana jin yaren Hausa. Tun loton baya, fina finan Hausa suka mamaye kasar Hausa da makwaftanta, tun ana yi a dabe har kawo yanzu da ake yinsa a talabijin.

Sai dai, tambayar da kowa yake yiwa kansa a kullum itace: Me ya sa ake kiran masana'antar shirya fina finan Hausa "Kannywood"?. Domin nemo sahihiyar amsar wannan tambayar, wakilan Legit TV Hausa suka yi tattaki zuwa jihar Kano, inda suka zanta da jarumi Ali Nuhu da Rabiu Daushe da wasu jaruman, kan sanin dalilin kiran wannan masana'anta Kannywood.

Ga bidiyon nan kasa domin jin Dalili daga bakin jaruman


Share this


Author: verified_user

0 Comments: