Saturday, 5 October 2019
Bayan Aurena Ya Mutu sau Biyu, mutane suna Ta zargin cewa lalacewa zanyi - Laila Ali Othman

Home Bayan Aurena Ya Mutu sau Biyu, mutane suna Ta zargin cewa lalacewa zanyi - Laila Ali Othman
Ku Tura A Social Media

A wata hira da tayi da manema labarai Laila Ali Othman kawa a wajen Hadiza Gabon ta bayyana dalla-dalla dalilin da ya sanya aure baya tasiri a yankin Arewacin Najeriya, sannan kuma ta bayar da shawarwarin da suka kamata

A wata hira da aka yi da shahararriyar matar nan da ta jajirce wajen taimakawa marayu da marasa galihu, wato Laila Ali Othman, ta bayyanawa wakilan BBC yadda mutane suka dinga yin wani tunani a kanta a lokacin da ta baro gidan mijinta na karshe.

Laila dai aminiya ce a wajen fitacciyar jarumar nan ta Kannywood, wato Hadiza Gabon. Laila ta yi aure har sau biyu amma Allah bai yi auren na ta za su dore ba, inda daga karshe take rabuwa da mazajen na ta.

A hirar da tayi da 'yan jarida Laila ta bayyana cewa lokacin da ta bar gidan mazajenta mutane da dama suna yi mata kallon cewa lalacewa za ta yi.

Ga dai abinda Laila ta ce a hirar da suka yi:

"Lalacewa ba aure ba ne ko kuma rashin aure, kai ne a matsayinka na mutum zaka ga abinda ya kamace ka. Iyaye na sun bani tarbiyya ta addinin Musulunci, na samu ilimin boko, Allah kuma yana taimako na ina cigaba da abinda nake yi.

"Sunana Laila Aliyu Othman, mutuwar aure biyu da ya same ni ya kara mini karfin gwiwa, zan iya shiga kowacce irin matsala na fita, kuma na ga mutane da yawa suna cikin matsala da damuwa, ga kashe-kashen mutane da ake ta faman yi yanzu, kaji ance mace ta kashe mijinta, duka hakan yana faruwa ne saboda basu da inda za su je su zauna su ji shawarwari.

"Da ki zauna a gidan miji ki yi ta aikata zunubi, saboda idan kika zauna kina yi mishi abinda ba ya so shima yana yi miki abinda baki so, kuna zagin juna, baya baki hakki baki bashi hakki to ina ganin ba aure kuke yi ba. Aure lada ake samu ba zunubi ba.

"Irin wadannan abubuwa abin kunya ne a Arewacin Najeriya, mutane ba su so suyi magana a kai bayan abin ya zo yayi mana katutu ya cinye mu, muna nan muna ji muna ganin al'ummarmu tana faduwa tana zama wani abu daban.
"Saboda haka dole ne mutane su gane cewa aure ba shine farko da kuma karshen rayuwarmu ba."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: