Wednesday, 23 October 2019
Ba Mu yi Wata Gwamnati Ba Sai Ta APC - Bello Muhammed Bello

Home Ba Mu yi Wata Gwamnati Ba Sai Ta APC - Bello Muhammed Bello
Ku Tura A Social Media
Shafin Northflix ya wallafa ,FitatcenJarumin Finafinan Hausa Bello Muhammed Bello wanda akafi sani da General Bmb Mazauni Jihar plateau (Jos). Yayi korafi ga Gwamnati akan yanda ake cin zarafin mutane ana Sara suka da kwacen kudade da wayoyi  a jihar ta plateau (jos).

Jarumin wanda yake shugabanta wata kunyar Masu goyawa shugaban kasa Muhammad Buhari Baya Mai Suna "Vote Buhari Again" (VOBA) tun lokacin kamfe. Yayi kiran ne Akan cewa Ya kamata Gwamnati ta yiwa tufkar hanci akan irin wannan wasa da rayuka da ake a jihar ta plateau (jos) da ma sauran jihohin da hakan ke faruwa a fadin kasar nan baki daya.

Abinda akayi ranar Lahadi a stadium din jihar plateau (Jos) yayi muni matuka, Yan Sara suka sun tare mutane a hanyar su ta fita suna dukan su, suna sara, suna masu kwace.

Har  saida muka fita nida mutane na muka yi artabu da wasu daga cikin yan ta`addan mukaci kaniyar su, amma duk da haka babu wasu Jami`an tsaro da suka zo. Inji BMB.

Na fito nayi magana da babbar murya!! har saida aka rika kirana a waya, ciki masu kiran kuwa harda ma haifina sakamakon irin fusatar da nayi.

Gaskiya ya kamata Gwamnati tasan halin da ake ciki saboda ba muyi wata jam,iyya ba Sai APC tun daga sama har kasa. Inji BMB.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: