Monday, 21 October 2019
Amal Umar Jarumar Da 'Yan Kudu Suke Amfani Da Ita Don Cin Fuskar Hausawa

Home Amal Umar Jarumar Da 'Yan Kudu Suke Amfani Da Ita Don Cin Fuskar Hausawa
Ku Tura A Social Media

Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Jaruma mai tasowa Amal Umar za a iya cewa ita kadai ce jarumar da take fitowa a finafinan kannywood kuma lokaci guda aka ga ta shahara a cikin finafinan kudancin kasar nan.

Yarinya ce'yar shekaru 20 wadda ta kware sosai wajen yin aktin, ga shi kuma idan tana yin turanci sai abin ya ba ka mamaki hakan ya ba ta damar samun waje a cikin finafinan da ake yi a kudu wanda ya shahara da sunan finafinan Nollywood don ta yi finafinai baya ga na Hausa akwai na turanci da suka hada da MTV Sugar, Wings of a Dove.

Wannan ce ta sa muka tambayi jarumar dangane da rawar da take takawa a cikin finafinan Hollywood  da kuma irin kallon da ake yi wa duk wani jarumin Hausa da yake fitowa a finafinan kudancin kasar nan in da take cewa.

To ni dai abin da na sani kuma zan iya magana shi ne ko a fim din Hausa ana zagin mu ana ce mana 'yan iska ne mu, wanda kuma  mutane suna mantawa  da cewa tarbiyya fa tarbiyya ce , duk yadda ka taso a gidan ku  a haka za ka rinka rayuwa a waje.

To ni dai na taso a gidan tarbiyya kuma ko na gama wannan fim din ban fuskanci kalubale ba , saboda duk inda na je ina tunawa da cewa ni musulma ce".

Ta ci gaba da cewa " kuma finafinan kudu ko yaushe aka kira ni zan yi a yanzu ma ina da finafinai da yawa wadanda suke kan hanyar fitowa wasu ma za a rinka haska su a tashar Arewa 24 nan ba da dadewa ba kuma yawancin finafinan kudu ana kira na ne ina fitowa a matsayin wadda za su iya sanyawa ta yi wani abu da ya shafi rayuwar Bahaushe.

Kamar auren wuri da ake yi mana , Dora wa yara talla da kuma auren dole , to duk irin wadannan finafinan su ne ake kira na, don haka ko gobe ko jibi aka kira ni zan je na yi".

Daga karshe ta yi kira ga masu yi mata kallon ba ta yi abin da ya dace ba to su yi mata kyakkyawar fahimta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: