Tuesday, 22 October 2019
An Fara Surutai Akan Kungiyar Mata 'Yan Fim

Home An Fara Surutai Akan Kungiyar Mata 'Yan Fim
Ku Tura A Social Media

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Tun bayan fitowar sabuwar kungiyar mata'yan fim mai sunakannywood Women Association of Nigeria, aka fara surutai dangane da fitowar kungiyar da kuma matan da suka hadu suka Samar da ita kungiyar.

Surutan ya fi fitowa daga mata 'yan fim saboda an alakanta kungiyar da mata, don haka kungiyar ta mata ce zalla ba namiji a cikin ta.

Maganar da ake yi a kan kungiyar ya samo asali ne daga irin yadda zubin shugabancin kungiyar ya kasance, domin kuwa idan an duba matan su sha biyu da suka hadu suka kafa ta , mafi yawan su 'yan a bi yarima ne a sha kida amma dai kai tsaye ba za ka kira su da sunan 'yan fim ba, don kuwa da yawan su ko da mutum yana cikin harkar fim din to sai ka yi masa dogon bayani kafin wasu daga cikin wadanan mata da kuma yadda aka yi suke 'yan fim a halin yanzu.

Misali idan muka duba ita Shugabar kungiyar ta riko Hauwa Aminu Bello ' yar fim ce amma fa irin wadda a cikin harkar fim ake kiran su da 'yan bayan kyamara, domin ita aikin ta tace hotuna da kuma hada su wato Editin, don haka idan ba dan cikin harkar ba to duk irin dogon bayanin da za ka yi wa mutum ba lallai ba ne ya gane ta.

A cikin kunshin shugabancin akwai Zahra'u Shata wadda akalla ta kusan shekara sha shida rabon ta da ya yi don tun lokacin da ta yi aure , sai kuma Rashida Adamu Abdullahi wadda ake ganin harkar fim ta yi mata saki uku tun shekarun da suka gabata, don haka sai ta ga babu mafita sai dai ta shiga harkar siyasa, don a yanzu ba ana kallon ta a matsayin 'yar fim ba ne ana yi mata kallon 'yar siyasa ce.

A cikin jarumai akwai Saratu Gidado da Asma'u Sani da Ladidi Tublas da Safiya Kishiya wadanda dukkan su suna cikin harkar ne amma tun tuni harkar ta yi jifa da su.

Ciki. Furodusa akwai Aisha Tijjani wada a baya ta yi suna sosai da kamfanin ta na Amat , amma dai a yanzu babu wani motsi da take yi , sai kuma Maryam Saleh Fantimoti mawaki da ita ma ta zamo a cikin kunshin shugabancin, sai kuma Maryam Kofar mata wadda ta yi wani fim guda daya tun sama da shekara sha uku da suka wuce, don haka ma ko a cikin 'yan fim ba kowa ya san ta ba.

To irin wannan kunshin shugabancin shi ne ya sa wadanan mata suka fito da wannan kungiyar a daidai lokacin da ita kanta masana'antar ba ta San inda ta sa gaba ba? don haka ne mutane suke yin korafi tare da tambayar cewar an ya kuwa wannan kungiyar ba da wata manufa aka kafa ta ba?

Me ya sai sai wasu baki ne za su zo su tagoranci harkar da sunan 'yan fim? Ko dai wata manufa ce da suke da ita suke neman damar ta wannan hanyar?

To yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda kungiyar za ta Samar wa kanta mafita dangane da irin kallon da ake yi musu, kuma lokaci da yanayi ne kawai zai tabbatar da hakan.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: